Gwamna Buni ya rushe majalisar zartarwa ta jiha, ya kori kwamishinoninsa

1
448

Gwamnan Jihar Yobe, Hon Alhaji Mai Mala Buni CON, ya rusa majalisar zartarwa ta jiha tare da sauƙe duk wasu masu muƙamai na siyasa daga ofisoshinsu a faɗin jihar.

A wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labarai na gwamnan Yobe, Mamman Mohammed, ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa sakataren gwamnatin jihar (SSG) ya bayar da umarnin kowane kwamishina ya miƙa sha’anin gudanar ofishinsa ga sakatarensa na dindindin.

Hakazalika, an umurci shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da ya miƙa shi ga babban jami’i a gidan gwamnati.

An umurci manyan sakatarorin dindindin a ma’aikatu daban-daban da su kula da harkokin ma’aikatun su.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Buni ya rantsar da sakatarorin dindindin guda biyu tare da babban mai binciken kuɗi

A wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labarai na gwamnan Yobe, Mamman Mohammed, ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa sakataren gwamnatin jihar (SSG) ya bayar da umarnin kowane kwamishina ya miƙa sha’anin gudanar ofishinsa ga sakatarensa na dindindin.

Hakazalika, an umurci shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da ya miƙa shi ga babban jami’i a gidan gwamnati.

An umurci manyan sakatarorin dindindin a ma’aikatu daban-daban da su kula da harkokin ma’aikatun su.

Sai dai kuma tsohon sakataren gwamnatin jihar wanda shi ne Shugaban kwamitin ƙaddamar da shi da sauran membobi za su ci gaba da zama shugaba da membobin na kwamitin har sai an rantsar da su a ofishin mai girma gwamna da mataimakinsa.

Gwamna Buni ya yabawa membobin majalisar zartaswa da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa bisa yadda suke yi wa jihar hidima tare da bayar da gudumawar nasarorin da gwamnatinsa ta samu.

Gwamna Buni ya yi musu fatan samun nasara a harkokinsu na gaba.

1 COMMENT

Leave a Reply