Gwamnatin Najeriya ta rabawa mutane 160,572 naira biliyan 14.6 a jihohin arewa shida

0
225

Shugaba na ƙasa, na ‘COVID-19 Action’ da Farfaɗowa fa Tattalin Arziƙi, (NG-CARES), Abdulkarim Obaje, ya ce Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira biliyan 14.6 a cikin shirin ga mutane 160,572 da suka ci gajiyar shirin a jihohin Arewa shida.

Da yake jawabi a Bauchi a ranar Laraba a ƙarshen taron majalisar ministocin birnin, Obaje ya ce asusun na cikin bashin dala miliyan 750 da Bankin Duniya ya samu a shekarar 2021 wanda ya kai 2023.

An shirya taron ne ga waɗanda suka ci gajiyar shirin a jihohin Bauchi, Gombe, Katsina, Jigawa, Kano da Filato.

Mista Obaje ya ce an ware wa kowacce jiha dala miliyan 20 yayin da babban birnin tarayya da NG-CARES suka samu dala miliyan 15 kowanne.

Ya ƙara da cewa dubun dubatar ƙanana da matsakaitan masana’antu ne suka amfana da shirin domin daƙile tasirin cutar ta COVID-19.

KU KUMA KARANTA: MSSN ta yi ƙorafi ga gwamnatin Najeriya akan rubuce-rubucen jima’i a cikin littattafan ‘yan firamare

Ya ce jihar Bauchi ta samu naira biliyan 4.2; Jihar Gombe ta samu naira Biliyan 3.3, Jihar Katsina ta samu naira Biliyan 3.04, Jihar Kano ta samu naira Biliyan 1.6, Jigawa ta samu naira Biliyan 1.4, Filato ta samu naira Biliyan 1.081.

A nasa jawabin, Rabaran Aso Vakporaye, shugaban kwamitin kula da fasaha na tarayya na N-G CARES wanda ya wakilci Ƙaramin Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare Tattalin Arziƙi, Mista Clem Agba, ya ce annobar COVID-19 ta lalata tattalin arziƙi da dama.

Ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya ta fitar da wasu tsare-tsare da dama a ƙarƙashin shirin Ɗorewa Tattalin Arziki, ESP, don daƙile tasirin cutar kan ƙananan ‘yan kasuwa.

Matakan, in ji shi, sun kuma shafi manoman waɗanda suka dogara da kuɗin abinci na yau da kullum don tsira.

“A cikin watan Yuli, ESP ta tsara tsare-tsaren don tattara kuɗaɗe da sauran albarkatu don tabbatar da daidaiton tattalin arziƙi, inganta kuɗaɗen shiga na man fetur da na gwamnati da kuma rage kashe kuɗaɗe marasa mahimmanci.

“Gwamnatin Tarayya ta sami damar lamuni na Bankin Duniya don haɓaka shirinta a ƙarƙashin ajandar kariyar zamantakewa da kuma ba da amsa cikin sauri da dacewa ga ƙalubalen da COVID-19 ke haifarwa.

“An samu lamunin dala miliyan 750 a madadin Jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja domin bunƙasa tattalin arziƙin cikin gida da kuma ƙara yawan amfanin gida a tsakanin talakawa da marasa galihu,” inji shi.

Leave a Reply