Majalisar dokokin Kano ta amince da dokar kare haƙƙin yara

1
245

A ranar Laraba ne majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar kare haƙƙin yara ta jihar.

An zartar da ƙudurin dokar ne bayan tattaunawa mai zurfi da kwamitin majalisar ya yi a yayin zaman majalisar wanda mataimakin kakakin majalisar Kabiru Dashi (APC-Ƙiru) ya jagoranta a Kano.

Bayan kammala tattaunawa ne ‘yan majalisar suka amince da karatu na uku na ƙudirin da magatakarda Garba Gezawa ya yi.

KU KUMA KARANTA: Hukumar FRSC ta nemi a kafa dokar shari’ar musulunci ga direbobi masu tuƙin ganganci

Jim kaɗan bayan zartar da ƙudirin dokar, mataimakin shugaban masu rinjaye, Ɗahiru Zarewa (APC-Rogo) ya ce an yi la’akari da shi kuma aka amince da shi bayan an gudanar da ayyukan majalisa daban-daban.

Ya ce an amince da dokar ne saboda jajircewar da ‘yan majalisar suka yi na bunƙasa yara da ci gaban jihar.

“A matsayinmu na wakilan jama’a, mu ne ke da alhakin samar da dokokin gudanar da shugabanci nagari a jihar,” inji shi.

Zarewa ya yabawa ’yan ƙungiyar bisa shigar da masu ruwa da tsaki waɗanda suka ba da gudumuwarsu ga ƙudirin.

A cewarsa, dokar idan aka sanya hannu kan dokar za ta inganta ilimi da duba ayyukan cibiyoyin marayu da kuma batun cin zarafin yara.

Majalisar ta kuma yabawa abokan aikin raya ƙasa bisa goyon bayan da suka bayar wajen ganin an samu nasarar zartar da ƙudirin.

Hakazalika, majalisar ta zartar da ƙudurin dokar asusun kula da tituna na jihar Kano, 2023. Shima da yake jawabi mataimakin shugaban majalisar ya bayyana cewa ƙudirin dokar na da nufin tallafawa hukumar kula da hanyoyin karkara ta jihar.

Ya kuma ce hakan zai taimaka wajen samar da kuɗaɗen gina hanyoyin shiga karkara. “Hukumar, idan aka kafa ta, za ta sauƙaƙe tare da inganta zamantakewar al’umma da tattalin arziƙin jama’a, musamman mazauna yankunan karkara da suke gudanar da ayyukan noma,” inji shi.

Wakilan haɗin gwiwar Ilimin ‘Yan Mata, Kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya, FOMWAN, NAPTIP da Hukumar Kare Yara ta Ƙasa, waɗanda suka yi jawabi bayan amincewa da ƙudirin, sun yabawa ‘yan majalisar kan ƙoƙarinsu.

Sai dai sun roƙi gwamnan da ya sanya hannu a kan ƙudirin dokar.

1 COMMENT

Leave a Reply