Gwamnatin jihar Kano ta bayyana wani yunƙuri da kafafen sada zumunta na yanar gizo ke yi a ƙasar, mai ɗauke da wani labari daga wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Ibrahim Kabiru Masari wadda ta shafi alaƙarsa ta siyasa da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na Jihar, Malam Muhammad Garba ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar asabar, ya bayyana cewa mummunar manufar yaɗa faifan bidiyon da aka ce na hannun wasu ‘yan kwangila ne da ke ƙoƙarin warware abin da ake ƙira ‘tattaunawa’ da nufin haifar da rikici, rashin jituwa tsakanin ‘yan siyasar biyu.
KU KUMA KARANTA: Za mu kawo ƙarshen shan miyagun ƙwayoyi a Kano – Ganduje
Ya bayyana cewa daga dukkan alamu wasu mutanen da ba su ji daɗin alaƙar Tinubu, Ganduje da Masari ba sun duƙufa wajen amfani da lamarin don amfanar da su.
Malam Garba ya kuma ƙara da cewa tun daga lokacin da gwamna da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar suka fahimci wannan mummunar yunƙuri na haifar da rashin jituwa a tsakaninsu, kuma ba za su bari wannan kyakkyawar alaƙa ta aiki da ta ƙara ƙarfi ba musamman a wannan mawuyacin lokaci da wasu masu son kai suka lalata ɗaiɗaikun mutane.
Kwamishinan ya yi ƙira ga ‘ya’yan jam’iyyar APC da sauran jama’a da su yi watsi da irin wannan yunƙurin kuma su kwantar da hankalinsu da biyayya ga jam’iyyar domin ganin an yi nasarar rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.