Kashe mutane 10 a Yobe: Haƙiƙanin abin da ya faru – daga wanda ya tsira da harbi

0
417

Daga Ibraheem El-Tafseer

A cikin watan Ramadana ne da ya gabata, al’ummar garin Buni Gari dake ƙaramar hukumar Gujba a jihar Yobe, suka wayi gari da mummunan labari na kashe magidanta mutane 10 rigis, ‘yan cikin garin. Abin ya faru ne ranar 14/4/2023. Wannan al’amari ya gigita al’ummar garin, kasantuwar yadda aka kawo gawarwakinsu kowane ɗauke da harbi a jikinsa.

Wakilin garin, wanda ake ce masa Wakili Kayama, ya shaida wa wakilinmu cewa “yadda dai rahoto ya zo mini shi ne, shi mutum na farko ɗin da aka fara kashe wa, ya tafi daji ya saro itace ya kawo gida, sai ya ƙara koma wa dajin, zai sake saro wani itacen. To a koma wa na biyun ne, sai suka haɗu da waɗannan yaran (‘yan Boko Haram). Da suka haɗu ba a san me ya faru ba, shiru har dare ya yi bai dawo ba. Har gari ya waye bai dawo ba. Sai mutanen gari suka tafi, za su dubo me ya faru da shi, ko rashin lafiya ko wani abu”.

“Sai mutane 10 suka tafi dajin don dubo halin da yake ciki. To ashe shi na farkon yaran (Boko Haram) sun kashe shi, su kuma mutane 10 da suka je dubo halin da yake ciki, sai suka kama su, suka ɗaure su, suka harbe su duka. To a cikinsu ɗaya bai mutu ba. Ya tsira da harbi a jikinsa. Idan ka haɗa da na farkon, da waɗannan guda tara, sun zama 10 kenan suka kashe”.

KU KUMA KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun kashe mutum ɗaya, sun yi garkuwa da uku a Kwara – ‘Yan sanda

“Sojoji da ‘yan Banga (vigilante) sune suka je dajin suka ɗebo gawarwakinsu, suka kawo min su. ‘Yan’uwansu suka zo, aka musu jana’iza. Akwai wanda ‘ya’yansa uku ne a ciki, duka an kashe su. Akwai wanda ‘ya’yansa biyu aka kashe. Shi wanda ya tsira da harbi ɗin, an kaishi Asibiti an masa magani, yanzu haka an dawo da shi gida” inji wakili Kayama.

Sunayen waxanda aka kashe ɗin, sun haɗa da Ibrahim Umar, Abdullahi Umar (Mala Ciyaman), Kachallah Lamba Kolo, Baba Ibrahim Manga, Babangida Muhammad Mamman, Bah Yarima, Alhaji Baba Grema, Abubakar Grema da Abbati Grema.

Wanda ya tsira da harbi ɗin, mai suna Ali. Akan idonsa aka yi komai, ya shaida wa wakilinmu cewa “ranar Alhamis, 14/4/2023 shi wannan ɗan’uwan namu da ƙaninsa, suka tafi daji saro itace. Bayan sun saro itacen sun kawo gida, to itacen da suka sara a dajin yana da yawa. Sai shi wannan ƙanin nasa yace bari ya koma dajin ya ɗebo ragowar itacen. Ya isa dajin, har ya ɗebo itacen yana hanyar fito wa daga dajin zai taho gida, sai ya ci karo da waɗannan yaran (‘yan Boko Haram) take suka kashe shi, suka ɓoye gawarsa”.

“Suka kwana a dajin suna jiran waɗanda za su zo nemansa. A gida an ga shiru bai dawo ba, har magariba ta yi, har dare ya fara shiru bai dawo ba. Kuma ga shi ana Azumi, bai dawo ya sha ruwa ba. Dole aka haƙura har zuwa wayewar gari. Da safe sai aka shirya za’a tafi dajin nemansa, saboda ba a san me ya hana shi dawowa ba. Rashin lafiya ne ko kuma juyewar kai. Kafin mu tafi dajin, sai muka je muka sanar da Sojojin dake garin abin da ke faruwa, akan ko za mu tafi tare cikin dajin, sai Sojojin suka ce ba za su samu zuwa ba. Sannan muka je wajen ‘yan Banga (vigilante), su ma suka ce mana ba za su samu zuwa ba”.

“To mun sanarwa jami’an tsaro sun ce ba za su je ba, mu kuma ba za mu bar ɗan’uwanmu a daji ba mu san halin da yake ciki ba. Shi ne muka shirya muka shiga dajin nemansa. Bayan mun shiga dajin, ni suka fara kama wa, suka ɗaure ni, suka ɓoye ni a wata duhuwa. Sai ɗayansu ya hau saman bishiya, ya ce ga can wasu mutanen gari da yawa suna taho wa. Sai suka ɓuya a bayan bishiyoyi. Sun ɗana tarkon kama duk wanda ya shigo. Duk wanda ya shigo dajin sai su kama shi, haka suka yi ta yi har sai da suka kama mu duka. Suka ɗaure mu, suka mana duka. Sai suka jera mu, suka buɗe mana wuta. Ba wai sun harbe mu ne ɗaya bayan ɗaya ba, a’a sun buɗe mana wuta ne”.

“Sai suka ce shikenan, mu tafi, mun kashe su, kafirai. Sai suka juya suka tafi abin su. To mu biyu ne ba mutu ba nan take. Akwai ɗayan, shi an harbe shi a ciki ne, bai mutu ba nan take, sai ya rarrafo, ya taho inda nake. Da yake ni harbin a ƙafa ya same ni (a cinyata). Da ya rarrafo sai ya sunce ni da bakinsa (da yake sun ɗaure hannayenmu ta baya), sai ni ma na sunce shi. Sai muka fara tafiya muna faɗuwa, muna ta tafiya muna faɗuwa, har shi wanda aka harba a cikin ya ka sa tafiya, ya faɗi a hanya ya qarasa cika wa (ya rasu). Ni kuma na samu na taho bakin gari. Sai na samu mutanen gari da yawa sun fito sun tsaya, saboda sun ji ƙarar harbin. Na gaya musu abin da ya faru, shi ne aka sake koma wa wajen jami’an tsaron, aka gaya musu abin da ya faru, shi ne suka tafi dajin suka ɗebo gawarwakin. To wannan shi ne haqiqanin abin da ya faru” inji Ali, wanda ya tsira da harbi.

Leave a Reply