Sojojin Isra’ila sun kashe ‘yan jarida 20 cikin shekara 21

0
222

Wata ƙungiya mai rajin kare lafiyar ‘yan jarida ta ce jami’an tsaron Isra’ila sun kashe ‘yan jarida aƙalla 20 tun daga shekara ta 2001, inda ta zargi sojojin ƙasar da ƙoƙarin kauce wa bincike.

Rahoton ƙungiyar ta ‘Committee to Protect Journalists’ ya bayyana gazawa wajen gudanar da bincike yadda ya kamata a kan irin waɗannan kashe-kashe.

KU KUMA KARANTA: Ranar ‘yan jarida ta ƙasa: Za mu bada goyon baya wajen yaɗa sahihancin labarai da kare ‘yancin ‘yan jarida – Kwamared Rajab

Kuma a yanzu ƙungiyar na hanƙoron ganin an gudanar da bincike na zargin aikata miyagun laifuka a kan aƙalla uku daga cikin kisan na ‘yan jarida.

Sai dai sojin Isra’ilar sun ce suna martabawa tare da tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida kuma ba sa harin ‘yan jaridar.

Leave a Reply