Masar ta buɗe iyaka ga ‘yan Najeriya da suka tsere daga Sudan

Gwamnatin tarayya a ranar Litinin ɗin da ta gabata ta tabbatar da cewa a ƙarshe gwamnatin Masar ta buɗe kan iyakokinta domin baiwa ‘yan Najeriya da ke tserewa daga Sudan da yaƙi ya ɗaiɗaita su ratsa cikin ƙasarta.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa gwamnatin Najeriya ta shirya tsaf domin jigilar ‘yan Najeriya daga Sudan zuwa Masar saboda rufe sararin samaniyar ƙasar.

Sai dai mutanen da aka kwashe sun maƙale a kan iyakar Masar na tsawon kwanaki saboda ƙin amincewa da ƙasar ta ba da izinin wucewa duk da tsoma bakin da tawagar Najeriya ta yi a Masar.

Ƙasar ta nace cewa dole ne kowa ya bi ƙa’idar biza ta al’ada kafin ya keta kan iyaka. A ranar Litinin ɗin da ta gabata ce shugabar hukumar kula da harkokin ƙasashen waje ta Najeriya NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce ƙasar da ke Arewacin Afirka ta amince da buɗe kan iyakokinta ga ‘yan Najeriya bayan shigar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta bayyana kashe dala miliyan 1.2 wajen ɗaukar motocin bas don kwashe ‘yan ƙasar daga Sudan

Ta ce Buhari ya tattauna da takwaransa na Masar, Abdel Fattah El-Sisi, kafin a cimma matsaya.

Shugaban NIDCOM, ya ce gwamnatin Masar ta amince da buɗe iyakar a ƙarƙashin wasu tsauraran sharuɗɗa. “Yanzu an buɗe kan iyakar, (tare da tsauraran sharuɗɗa) bayan da Shugaba Buhari ya shiga tsakani da Shugaban Masar.

Don haka za a fara aikin jigilar mutanen da ofishin jakadancin Najeriya da ke Masar zai yi,” inji ta.


Comments

One response to “Masar ta buɗe iyaka ga ‘yan Najeriya da suka tsere daga Sudan”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Masar ta buɗe iyaka ga ‘yan Najeriya da suka tsere daga Sudan […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *