No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani gida da ke cikin harabar fadar Ooni na Ife, Adeyeye Ogunwusi, Ojaja II, ya kama da wuta da misalin ƙarfe 11:30 na dare ranar Juma’a.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin fadar, Moses Olafare, ya fitar ranar Asabar, a Ile-Ife.

‘Yan sandan sun bayyana cewa wutar ta tashi ne sakamakon tashin wutar da ta tashi ta na’urorin lantarki a gidan da abin ya shafa.

A cewarsa, gobarar ba ta ba zu ba bayan ginin da abin ya shafa da ke wani sashe na harabar fadar.

KU KUMA KARANTA: Kimanin shaguna 50 ne gobara ta cinye a kasuwar Singa

Ya ci gaba da cewa, an kashe gobarar cikin gaggawa ta hanyar haɗin gwiwar hukumar kashe gobara ta gwamnati, hukumar kashe gobara ta OAU da sashin bayar da agajin gaggawa na fadar.

Ya yi godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da cewa ba a samu asarar rai ba, ba a samu rahoton jikkata ba, ba a yi asarar kayayyakin al’adu ba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

1 COMMENT

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...