‘Yan sanda sun kwato bindigogi ƙirar AK-47 guda huɗu a Kano

1
310

Jami’an ‘yan sanda a jihar Kano sun kama bindigogi ƙirar AK-47 guda huɗu daga hannun wasu masu laifi a hanyar Kano zuwa Bauchi a ranar 25 ga watan Afrilu.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kakakin rundunar ‘yan sandan Kano SP Abdullahi Kiyawa a ranar Juma’a.

Ya ce, tawagar ‘yan sintiri na babbar hanya ta ‘Safer’ ce ta ƙwato bindigogin a yayin da suke gudanar da bincike bisa jagorancin sirri a Kwanar Garko da ke ƙaramar hukumar Garko.

“A yayin samamen da jami’an ‘yan sandan suka yi a kan hanyar Kano zuwa Bauchi, ‘yan sandan sun hango wata motar bas ta ‘Liter-Hiace’ tana ƙoƙarin sauya alƙibla inda ɗaya daga cikin mutanen ya sauko yana riƙe da wani abin tuhuma.

KU KUMA KARANTA: PSC ta amince da korar jami’an ‘yan sanda 3, ta kuma rage ma’aikata 5 daga aiki

“Wannan matakin ya jawo hankalin tawagar cikin gaggawar mayar da martani, wanda ya tilasta wa wanda ke cikin motar ya jefar da abin, ya yi nisa kuma ya tsere daga wurin,” in ji kakakin rundunar.

Ya ƙara da cewa, binciken da aka yi wa buhun ya gano cewa tana ɗauke da bindigogin AK-47 guda huɗu. “Haka ɗin ya sa jami’an tsaro sun ƙara ƙaimi domin kamo waɗanda ake zargi da gudu,” in ji Kiyawa.

A cewarsa, muƙaddashin kwamishinan ‘yan sandan, Mu’azu Mohammed, ya yabawa jami’an da suka yi aiki mai kyau. Ya kuma buƙaci mazauna jihar da su ƙara taka tsan-tsan wajen tsaro tare da kai rahoton mutanen da suka yi zargin ko wani abu zuwa ofisoshin ‘yan sanda mafi kusa.

Mista Kiyawa ya ƙara da cewa “Suna iya bayar da rahoto ta lambobin gaggawa na rundunar: 08032419754, 08123821575, 0807609127 da 09029292926.”

1 COMMENT

Leave a Reply