No menu items!

Sample Page Title

Date:

A ranar asabar ɗin da ta gabata ne dakarun Operation Hadarin Daji suka kashe ‘yan ta’adda 7 tare da cafke wasu biyu tare da lalata wasu sansanonin su a ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Daraktan ayyukan yaɗa labarai na tsaro Musa Ɗanmadami ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Mista Ɗanmadami (Manjo Janar), ya ce sojojin sun samu wannan nasara ne a yayin wata arangama da ‘yan bindigar a garuruwan Birnin Tsaba, Tsanu, Lamba, Gabas, Gidan Kaso, da dajin Dumburum a ƙaramar hukumar Zurmi.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda 53, sun ceto 118

Ya ce sojojin sun ƙwato babura bakwai, da bindigogi ƙirar AK 47 da kuma gidan rediyon Baofeng guda ɗaya. A cewarsa, bayan kama wani ɗan ta’adda da aka yi a ranar 21 ga Afrilu, sojojin sun gudanar da wani samame tare da kama wasu ‘yan ta’adda biyu a garin Shinkafi da ke ƙaramar hukumar Shinkafi.

“Kayan da aka ƙwato daga hannun waɗanda ake zargin sun haɗa da babur ɗaya da wayoyin hannu guda uku. “Babban kwamandan sojojin ya yabawa sojojin na Operation HADARIN DAJI kuma suna ƙarfafa jama’a da su baiwa sojoji bayanai masu inganci kuma akan lokaci kan ayyukan aikata laifuka,” in ji shi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

3 COMMENTS

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...