Abin da ya sa gwamnatin Masar ta ce a koma cin ƙafar kaza a ƙasar

0
473

Ƙasar Masar na fuskantar wani matsanancin yanayin tattalin arziƙi, wani lamari da ya sa da ƙyar Misirawa ke iya ciyar da iyalansu.

Shawara ta baya-bayan nan kan abinci mai gina jiki da gwamnati ta bai wa ‘yan ƙasar ita ce cin ƙafar kaza. Wani sashen jikin tsuntsaye mai yawan sinadaran gina jiki, ko da yake, galibi ana zubarwa ne don karnuka da maguna su samu abin kalaci.

Wannan shawara ta fusata ‘yan ƙasar har ta kai ana kakkausar suka ga gwamnati.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Zulum ya tura marayu 19 koyon karatun likita a Masar

Ƙasashe da yawa na fama da gagarumar hauhawar farashi, sai dai duk da hauhawar farashin ta zarta kashi 30 cikin ɗari a wannan wata na Maris, Masar na cikin ƙasashen da suka fi jin jiki.

Ga mafi yawan mutane, kayan abincin da a baya kusan kowa yana iya saye, kamar man girki da cukwi amma sun fi ƙarfin mutane da yawa.

Farashin irin waɗannan kayan abinci ya ninka sau biyu ko sau uku a ‘yan watanni.

“Sau ɗaya nake cin nama a wata, ko kuma ba saye nake ba kwata-kwata.

Nakan sayi kaza sau ɗaya a duk mako,” in ji Wedad, wata mahaifiya mai ‘ya’ya uku da ke cikin shekarunta na sittin, a lokacin da take tafiya a tsakanin rumfunan kasuwa.

“A ‘yan kwanakin nan, ko ƙwai yana kai wa senti 16.”

Wani ɓangare na dalilin da ya sa Masar take fama shi ne ta dogara ne kacokan kan abincin da ake shiga da shi ƙasar daga ƙetare.

Maimakon noman da ake yi a cikin gida don ciyar da ɗumbin al’ummarta sama da miliyan 100.

Kai hatta hatsin da ake ciyar da kajin ƙasar shigar da shi ake yi daga waje.

Fiye da wata 12 da suka wuce, darajar kuɗin Masar wato fam ta faɗi da rabi idan an kwatanta da dalar Amurka.

A watan Janairu, lokacin da gwamnati ta sake rage darajar kuɗin, sai abin ya ƙara haddasa tsadar kayan da ake shigarwa kamar hatsi.

Ya Allah, Kada Ka bari mu shiga tsananin da zai kai mu ga cin ƙafar kaza,” in ji wani mai bara a gefen masu sayar da kaji cikin kasuwar Giza.

Leave a Reply