Shekaru 13 da aure, kotu ta raba su, saboda barazana ga rayuwar ta

1
529

Wata kotun al’ada mai daraja ta ‘A’ da ke Ibadan ta raba auren shekaru 13 da aka yi tsakanin Susan Udeze da mijinta, Frank bisa zargin barazana ga rayuwar ta.

Da yake yanke hukunci, shugaban kotun, S.M. Akintayo ya ce ya raba auren ne domin a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Misis Akintayo ya baiwa Udeze riƙon yaran biyu sannan ya umurci Frank ya dinga biyan N15,000 duk wata a matsayin alawus.

Ya umurci Udeze da Frank su kasance tare wajen karatun yaran da sauran jin daɗinsu. Shugaban kotun ya kuma ba da umarnin hana Frank musgunawa, barazana da kuma kutse ga rayuwar Udeze na sirri.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta raba auren ‘yar Ganduje da ya shafe shekaru 16

Ya umarci Ms Udeze da ka da ta hana Frank shiga wajen yaran.

“Frank ya kira ni mayya kuma ya kore ni daga gida da daddare bayan ya doke ni. “Ba yi mini ta’aziyya ba lokacin da mahaifiyata ta rasu. “Na ƙara tsorata da Frank lokacin da ya yi barazanar zuba mini ruwan acid.

Na kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda, na gudu daga gidansa,” inji ta. Sai dai wanda ake ƙara bai kasance a kotu ba lokacin da aka ƙira shi ya fara kare kansa.

1 COMMENT

Leave a Reply