An ɗaure mai sana’ar POS watanni uku a gidan yari kan satar N120,000

0
376

Wata kotun majistiri da ke Ota a Ogun, a ranar talata, ta yanke wa wata matashiya mai sana’ar POS (Point Of Sale), mai suna Salawudeen Ayomide, mai shekaru 22, hukuncin ɗaurin watanni uku a gidan yari bisa samunta da laifin satar Naira dubu 120,000 mallakin mai aikinta.

Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da Ayomide wanda ba a bayar da adireshinta da laifin sata ba, biyo bayan tuhumar ta da laifin da ta aikata.

A hukuncin da ta yanke, A. O. Adeyemi, ta baiwa mai laifin zaɓin Naira 3,000 sannan kuma ya umarce ta da ta biya N120,000 ga wanda ya shigar da ƙara, Nosiru Jayeola.

KU KUMA KARANTA: Yadda aka kama matashin mai damfarar masu POS

Tun da farko, mai gabatar da ƙara, Insp E.O. Adaraloye, ya shaidawa kotun cewa wanda ake tuhuma ta aikata laifin ne a ranar 8 ga watan Fabrairu da misalin ƙarfe 8 na safe, a unguwar Ogba Ayo, Ijoko a Ota.

Mista Adaraloye ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 390(9) na kundin laifuffuka, Vol.1, Laws of Ogun, 2006.

Leave a Reply