An saki tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa da aka sace

An sako Farfesa Onje Gye-Wado, tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa da wasu ‘yan bindiga suka sace ranar 7 ga watan Afrilu.

DSP Ramhan Nansel, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO, ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a ranar Litinin a Lafiya.

Kun tuna cewa Gye-Wado wanda ya kasance mataimakin gwamna tsakanin 1999 zuwa 2003 a gwamnatin Abdullahi Adamu, an yi garkuwa da shi a gidansa da ke ƙaramar hukumar Wamba.

KU KUMA KARANTA: Yadda ‘yan sanda suka ceto ɗan jarida daga hannun masu garkuwa da mutane

PPRO ya ce tsohon mataimakin gwamnan ya sami ‘yanci ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren Lahadi, kuma tuni ya koma cikin iyalansa.

Nansel wanda ya ce har yanzu ba a kama su ba, ya ƙara da cewa ‘yan sandan ba su da masaniyar wani kuɗin fansa da aka biya kafin a sako su.

A cewarsa, an saki dattijon ne saboda ci gaba da matsin lamba da haɗin gwiwar jami’an tsaro suka yi wa masu garkuwar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *