An kashe ɗalibin jami’a akan bashin naira dubu ɗaya

0
357

Wani sabon ɗalibi da ya kammala digiri a jami’ar Adekunle Ajasin Akungba, Akoko (AAUA), jihar Ondo, mai suna Temitayo, ya yanke jiki ya faɗi a kan bashin N1,000.

Rahotanni sun bayyana cewa, an caka wa marigayin wuƙa ne da Almakashi da sanyin safiyar ranar Alhamis, 6 ga watan Afrilu, a kusa da tashar mai na Ebenco, daura da mahaɗar Akua, Akungba.

An garzaya da Temitayo zuwa Asibitin Aduloju dake kan titin Iwaro inda daga baya ya mutu sakamakon raunin da ya samu. An tattaro cewa marigayi Temitayo wanda ya kammala karatunsa a sashen ‘Physics Electronics’ yana cikin makarantar yana jiran ya ƙare aikinsa.

KU KUMA KARANTA: Rikicin Kutep da Fulani, an kashe mutane 8 a Taraba

Majiyar ƙungiyar ɗaliban Jami’ar ta shaidawa Peoples Gazette cewa Temitayo ya shiga tsakani ne a rikicin biyan bashin naira dubu tsakanin wani “Egbon Adugbo” da kuma wani ɓangare na uku, inda ya yi alƙawarin sasanta ƙudirin na baya-bayan nan.

Temidayo dai ya iya biyan masu bashin naira 3000 daga cikin naira 4000 amma ya ka sa biyan sauran naira dubu ɗaya da ta rage wanda hakan ya haifar da cece-kuce da ya yi sanadiyar mutuwar ɗalibin da ya kammala karatun digiri.

“Wani mutum (na uku) yana bin su kuɗi,” in ji majiyar “kuma ya shaida musu (waɗanda suka aikata laifin) cewa zai taimaka wa mutumin ya biya kuɗin domin gudun kar ba a biya ba.

Don haka ya biya dubu uku daga cikin N4,000 kuma bai iya biyan sauran ba. Sai suka fara ta da masa hankali, sai ya ce su daina tayar masa da hankali, wai shi bai biya bashi ba, sai kawai ya taimaka, a biya, to sai aka fara cece-kuce, shi ne ya caka masa wuƙa, inda ya mutu nan take”

Leave a Reply