Ba zan saka Matana da ‘Ya’yana cikin Gwamnati ba – Abba Gida Gida

2
256

Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce matansa da ‘ya’yansa ba za su shiga gwamnati ba a harkokin mulkin jihar.

Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabin karɓar takardar shaidar lashe zaɓe. Ya ce, “matana ba za su shiga cikin harkokin mulki ba, haka suma ‘Ya’yana ba za su shiga cikin harkokin mulki ba.

KU KUMA KARANTA: Yadda Abba Kabir Yusuf na NNPP ya lashe zaɓen Kano

“Kuma zan iya gaya muku tabbas haka ne ga mataimakin gwamna na”. In ji shi.

Zaɓaɓɓen gwamnan ya kuma yi kira ga ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Nasir Yusuf Gawuna, da sauran ’yan takarar da suka fafata a zaben da aka yi a ranar 18 ga watan Maris, da su shiga gwamnatinsa domin gudanar da ingantaccen shugabanci a jihar.

2 COMMENTS

Leave a Reply