Kakakin majalisun jihar Yobe da Filato sun rasa kujerunsu

0
306

Daga Ibraheem El-Tafseer

Kakakin majalisar jihar Yobe Alhaji Ahmed Mirwa na jam’iyar APC ya rasa kujerarsa a zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha da aka gudanar a jiya Asabar 18 Maris 2023.

Lawan Mirwa shi ne ya ke wakiltar Nguru II (Nguru Outside) a Majalisar Jihar Yobe, tun daga shekarar 2003, ya shafe shekaru 20 a kan wannan kujera kenan. Amma ya faɗi a wannan zaɓe, inda dan takarar jam’iyar PDP, Musa Lawan Majakura ya yi nasara.

Majakura na PDP ya samu ƙuri’u 6,648. Mirwa na jam’iyar APC kuma ya samu ƙuri’u 6,466. Jatau na jam’iyar NNPP ya samu ƙuri’u 23. Mai Zare na jam’iyar APM ya samu ƙuri’u 14. Sai Isah Saidu Shehu na jam’iyar ADC ya samu ƙuri’u 30.

KU KUMA KARANTA: Jam’iyyun APC da NNPP sun umurci magoya bayansu da su tare a cibiyoyin tattara zaɓe a Kano

Shugaban tattara sakamakon zaɓe na Nguru II, Alhaji Mahdi Damaturu ne ya bayyana sakamakon zaɓen, inda Lawan Musa Majakura na jam’iyar PDP ya lashe zaɓen.

Majakura mai shekaru 29, yana da matakin karatu na Diploma, wadda ya yi ta Atiku Abubakar College of Legal and Islamic Studies.

Kakakin majalisar Jihar Filato, Yakubu Sanda shi ma ya rasa kujerarsa a zaɓen gwamnoni da na ‘yan Majalisar jiha da aka gabatar a jiya Asabar. ‘Yar takarar jam’iyar PDP Happiness Akawu ce ta yi nasara a zaben Pengana da ke karamar hukumar Bassa a jihar Plateau.

Sakamakon zaben wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta ayyana, ta bayyana Akawu ta jam’iyar PDP ta samu kuri’u 9, 926. Sanda (speaker) ya samu kuri’u 6,721.

Leave a Reply