Yadda mace ta kama azzakarin mai gidan da take haya, tayi ta ja har ya mutu

0
436

A ranar Asabar 11 ga watan Maris ne rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wata mata ‘yar shekara 33 mai suna Ifeoma Ossai, wacce ake zargi laifin kashe mai gidan da take haya, mai suna Monday Surulere Oladele mai shekaru 50, kan wata ‘yar taƙaddama.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya sanyawa hannu, ya ce an kama wacce ake zargin ne biyo bayan rahoton da wani Olaleye Taiwo ya gabatar a ofishin ‘yan sanda da ke sashen Sango Ota, inda ya bayyana cewa ɗan uwansa, Monday Oladele ya samu rashin jituwa da matar da ke haya a gidansa a kan biyan kuɗin wutar lantarki, ana cikin haka ne sai ‘yar hayar, wacce bata da miji amma tana da ɗa ɗaya, ta damko azzakarin marigayin, ta yi ta jan shi da ita.

KU KUMA KARANTA: Yadda wani mutum ya fille kan matarsa, ya sare hannun ‘yarsa

Sakamakon haka mai gidan ya faɗi ƙasa a sume kuma aka garzaya da shi babban asibitin Ota inda likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa.

Ifeoma, wacce ake zargi

“Bayan rahoton, DPO na Sango ota, CSP Saleh Dahiru, cikin gaggawa ya jagoranci jami’ansa zuwa wurin da lamarin ya faru, ba tare da ɓata lokaci ba aka cafke wanda ake zargin, aka kai shi gidan yari domin gudanar da bincike.

A yayin da ake yi masa tambayoyi, wadda ake zargin ta yi ikirarin cewa marigayiyar ya buƙaci ta biya kuɗin wutar lantarki, amma ta dage cewa har sai an haɗa ruwa kai tsaye zuwa shashin gidanta kamar yadda mai gidan ya alƙawarta kafin ta tare, ba za ta biya wutar lantarki ko wani kuɗin amfani ba har sai an haɗa mata wuta.

“Hakan ya haifar da hatsaniya a tsakanin su, sakamakon haka wacce ake zargin ta damke azzakarin marigayin ta yi ta jan shi da ita.

“Daga bisani marigayin ya faɗi, inda aka garzaya da shi asibiti amma likita da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwarsa. In ji kakakin ‘yan sandan.

Tuni dai aka ajiye gawar Marigayin a ɗakin ajiyar gawarwaki na asibiti domin ci gaba da bincike.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun, CP Frank Mba, ya bayar da umarnin miƙa wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da bincike.

Leave a Reply