Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tarwatsa sansanin ‘yan bindiga tare da ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a Zamfara.
Waɗanda abin ya shafa dai sun shafe kwanaki 68 a hannun masu garkuwa kafin daga bisani ‘yan sanda su kubutar da su.
A cewar rahoton da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), ya fitar a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ya fitar ranar Asabar a Gusau.
A cewarsa, “A ranar 10 ga Maris, 2023, jami’an ‘yan sanda tare da ’yan banga, yayin da suke aikin sintiri a kusa da dajin Munhaye, sun yi nasarar fatattakar wasu sansanin ‘yan bindiga mallakar wani sarkin ‘yan fashi da makami, wanda aka fi sani da Dogo Sule.
“Sakamakon aikin, an kubutar da mutane 14 da aka yi garkuwa da su, waɗanda suka hada da manya maza biyu, mata bakwai da yara biyar ‘yan ƙasa da shekara biyu.
KU KUMA KARANTA: Yadda ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da mutane 53, suka kashe mata masu juna biyu a wasu ƙauyuka huɗu a Neja
“Waɗanda abin ya shafa sun sanar da jami’an ‘yan sanda cewa, a ranar 1 ga watan Janairun 2023, da misalin ƙarfe 11 na dare , wasu da dama da ake zargin ‘yan bindiga ne ɗauke da manyan makamai, suka afkawa ƙauyukan Anguwar Mangoro da Gidan Maidawa a ƙaramar hukumar Gusau, suka yi awon gaba da wadanda abin ya shafa zuwa sansaninsu, inda suka shafe kwanaki 68 a tsare.
“Waɗanda lamarin ya rutsa da su suna cikin mawuyacin hali, kuma an kai su asibitin ‘yan sanda da ke Gusau domin kula da lafiyarsu, daga nan kuma aka haɗasu da ‘yan uwansu,” in ji Shehu.
Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Kolo Yusuf, ya taya waɗanda abin ya shafa murna domin samun ‘yancinsu, ya kuma ba da tabbacin ci gaba da jajircewar rundunar na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa.
[…] KU KUMA KARANTA: Yadda ‘yan sanda suka ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a Zamfara […]
[…] KU KUMA KARANTA: Yadda ‘yan sanda suka ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a Zamfara […]
[…] KU KUMA KARANTA: Yadda ‘yan sanda suka ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a Zamfara […]