No menu items!

Sample Page Title

Date:

Shahararren malamin addinin musulunci mazaunin jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi ya sanar da rasuwar mahaifiyarsa.

Rahotanni sun nuna cewa mahaifiyarsa ta rasu ne a ranar lahadin da misalin karfe 5:30 na yamma a wani asibiti da ke garin Abuja.

Ana shirye-shiryen binne ta a makabartar Unguwar Sarki da ke Kaduna a ranar Litinin 06/03/2023 bayan sallar Azahar a gidan marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi dake Unguwar Sarki GRA, bayan Lugard Hall a Kaduna.

KU KUMA KARANTA: An yi jana’izar babban ɗan Gwamnan Nasarawa da Allah Ya yiwa rasuwa

A wata sanarwa da Shaihin Malamin ya fitar a shafin sa na Facebook da aka tabbatar, Malamin ya ce: “Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun. A yau Lahadi da karfe 5:30 na yamma, ina sanar da rasuwar mahaifiyata.

“Don Allah ku nema mata gafara da rahamar Allah. “Kalmar da ta yi min sati biyu da suka wuce: lnsha Allahu, Allah zai haɗa ta da ‘ya’yanta da jikokinta a Aljannah”. (Da yardar Allah ta musamman, Allah zai haɗa ta da ‘ya’yanta da jikokinta a gidan Aljannah)” in ji Malamin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...