No menu items!

Sample Page Title

Date:

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP, Adewole Adebayo ya buƙaci Peter Obi na jam’iyyar Labour (LP) da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da su amince da shan kaye da nuna bajinta ta hanyar kiran ɗan takarar jam’iyyar APC Bola Tinubu ta wayar salula tare da taya shi murna.

Adebayo, a cikin wani sakon Twitter a ranar Talata, ya ce ya kamata Atiku da Obi su nuna son Najeriya ta hanyar amincewa da nasarar Tinubu.

Ya ce: “Chinua Achebe ya yi gaskiya cewa shugabanci shine matsalar Najeriya.

KU KUMA KARANTA: Yadda sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ya kasance a jihohin Edo, Akwaibom, Benue da Neja

“Ina shugabanni na gaskiya? Irin wannan wasan kwaikwayo a duk shekarar zaɓe ba a ci gaba,” Adebayo ya rubuta.

“Ina da ƙorafe-ƙorafe fiye da yadda duk ‘yan takarar shugaban ƙasa duka haɗu, ban gamsu da sakamakon ba, ni ban gamsu da zaɓen da aka yi ba.

“Haƙƙin mutane ne su yi zaɓukan da ba su dace ba amma zaɓin a bayyane yake, za mu iya zama masu gaskiya a ko’ina.” In ji shi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

3 COMMENTS

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...