Atiku ya doke Tinubu a Katsina, jihar Buhari

1
261

Jam’iyyar adawa ta PDP ta doke jam’iyyar APC mai mulki a jihar Katsina,jihar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya doke babban abokin hamayyarsa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC da ƙuri’u 489,045 a faɗin ƙananan hukumomi 34 na jihar.

Tinubu ya zo na biyu da ƙuri’u 482,045 a zaɓen da aka gudanar ranar Asabar. Jami’in zaɓen shugaban ƙasa na jihar Katsina Farfesa Mu’azu Abubakar Gusau ne ya sanar da sakamakon zaɓen da safiyar yau Litinin.

KU KUMA KARANTA: Atiku ya lashe zaɓe a mazaɓar elRufa’i da ta Ahmed Lawan

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso, ya zo na uku da ƙuri’u 69,385 sannan Peter Obi na jam’iyyar Labour ya zo na huɗuu da ƙuri’u 6,376.

Jami’in zaɓen jihar ya bayyana cewa an soke sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a wasu rumfunan zaɓe na ƙananan hukumomi 15 saboda ‘yan daba da kuma kada ƙuri’a da dai sauransu.

A zaɓen ‘yan majalisar dokokin jihar da aka gudanar a jihar, jam’iyyar APC mai mulki ta wanke dukkanin kujerun ‘yan majalisar dattawa uku da 9 daga cikin kujeru 15 na majalisar wakilai inda suka bar wa jam’iyyar adawa ta PDP da kujeru shida.

1 COMMENT

Leave a Reply