Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Laraba ta sanar da takaita zirga-zirgar ababen hawa a lokacin zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu daga karfe 12:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.
Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, a wata sanarwa, ya ce za a kiyaye dokar a duk faɗin ƙasar. Ya ce, duk da haka, ya ce dokar bata shafi waɗanda ke kan muhimman ayyuka kamar irin su jami’an INEC, masu sa ido kan zaɓe, motocin ɗaukar marasa lafiya da ma’aikatan kashe gobara da ke ba da agajin gaggawa.
Ya ce, takunkumin zai taimaka wajen tabbatar da tsarin tafiyar da jama’a yadda ya kamata, da kuma kare lafiyar masu zaɓe da kuma baiwa jami’an ‘yan sanda damar yin aiki mai inganci.
KU KUMA KARANTA: An tura masu hidimar ƙasa sama da dubu 200 aikin zaɓe
Ya ce sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba ya kuma hana mataimakan tsaro da masu rakiya ga shugabanninsu zuwa rumfunan zaɓe da wuraren tattara sakamakon zaɓen.
A cewarsa, duk wanda aka samu ya karya dokar za a saka masa takunkumi mai tsanani.
“Jami’an tsaro na musamman da aka sanya wa aikin zaɓe ne kawai za a gansu a ciki da wajen ɗakunan zaɓe da wuraren da aka keɓe.
“Haka kuma, dokar hana amfani da jiniya ba tare da izini ba, fitillu, rufaffiyar lambar mota, da gilashi mai duhu har yanzu yana kan aiki kuma za a hukunta masu karya doka yadda ya kamata.
“Haka kuma an hana duk jami’an tsaro na gwamnatocin jihohi da ƙungiyoyi da jami’an tsaro na sirri da masu gadi da jami’an tsaro tsaro masu zaman kansu shiga harkokin tsaron zaɓe,” inji shi.
IGP ya yi nadamar rashin jin daɗin da takaita zirga-zirgar zai haifar ga ‘yan Najeriya masu kishin kasa, ya kuma buƙaci masu zaɓe da su kasance masu bin doka da oda kuma su fito baki ɗaya domin yin amfani da damar su.
IGP Usman Alƙali Baba ya yi gargaɗin cewa rundunar za ta yi taka-tsan-tsan da duk wanda ke son gwada ƙudiri da ƙarfin ’yan sanda don ganin an gudanar da zaɓe cikin lumana.
Ya kuma umarci ’yan ƙasa da su guji siyen ƙuri’u ko sayar da ƙuri’u, kalaman ɓatanci, ba da labari da ƙarya, satar akwatunan zaɓe da kuma aikata sauran Laifuka.
Baba ya ce ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro za su tabbatar da cewa an gurfanar da duk waɗanda suka saɓa dokokin zaɓe, ya kuma buƙaci jama’a da su tuntuɓi ‘yan sanda da ɗakin gudanar da zaɓe na haɗin gwiwa da ke hedikwatar rundunar a Abuja, ta hanyar manhajar ‘NPF Rescue Me App’, da ke kan wayoyin Android da iOS.
Ya ce jama’a za su iya buga layin hukumar na NPF Rescue Me Emergency Toll kyauta, 08031230631 don kai rahoton mutanen da ake zargi, ko ayyukan da suka yi ko kuma neman ɗaukin tsaro.