Ba za a rufe Network saboda zaɓe ba- ACAMB

0
440

Ƙungiyar Manajojin Harkokin Kamfanoni na Bankuna (ACAMB), da ƙungiyar ƙwararrun masana harkokin sadarwa da kasuwanci da ke aiki a ɓangaren bankunan Najeriya tayi lurakan yadda ake ta yaɗa saƙwanni a kafafen sada zumunta na cewa babban bankin Najeriya CBN zai rufe ayyukan banki na tsawon kwanaki biyar daga ranar alhamis 23 ga wata zuwa litinin 27 ga watan Fabrairun 2023 saboda babban zaben da za a gudanar a Najeriya a ƙarshen mako biyu masu zuwa.

A wata sanarwar da Rasheed Bolarinwa Shugaban, Ƙungiyar Ma’aikatan Harkokin Kasuwanci na Bankuna (ACAMB) ya fitar ya kuma sanya wa hannu a ranar Laraba 22, ga watan Fabrairun 2023, ya ce ƙungiyar ta ACAMB na fatan ƙaryata labaran karya gaba ɗayansu tare da tabbatarwa ‘yan Najeriya da sauran al’umma masu ta’ammali da bankuna cewa babu gaskiya a cikin sakon da ake yaɗawa.

KU KUMA KARANTA:2023: El-Rufai ya yi gargaɗi kan amfani da ƙabilanci da addini wajen yaƙin neman zaɓe

“Har ya zuwa wannan lokaci, babu wani Bankin ajiyar (DMB) ko wasu cibiyoyi da ke ba da sabis na kuɗi da suka sami wani umarni ko sadarwa daga CBN na rufe kofofin bankunan su na zahiri ko kuma rufe hanyoyin sadarwar yanar gizo (dijital) da tashoshi na banki a kan abokan cinikin su saboda zabe.

“ACAMB na ƙara tabbatar wa abokan hulɗar su cewa bankunan nasu sun samar da matakan tabbatar da cewa masu ajiya za su iya shiga asusun ajiyar su kamar yadda suka saba a wannan lokaci.

“Hakanan, abokan cinikin da ke son aiwatar da canja wuri ko amfani da sabis na banki na lantarki za su sami damar shiga waɗannan ayyukan ba tare da cikas ba kafin, lokacin da kuma bayan zaɓe”. In ji shi.

ACAMB ta bukaci ‘yan Najeriya da kada su firgita su kuma kaucewa kashe kuɗi ba bisa ka’ida ba sakamakon labaran ƙarya da ake zargin an yi na rufe rassan bankuna da dukkan tashoshin banki na zamani.

Ya ce ya kamata jama’a su yi watsi da saƙon da ya taso daga mawallafinsa marasa fuska don haifar da rashin jituwa tsakanin ‘yan ƙasa da DMBs.

ACAMB ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su kasance cikin lumana da kwanciyar hankali a lokacin zaɓe tare da yi wa al’ummar ƙasar fatan samun nasarar gudanar da sahihin zaɓe da gaskiya.

Leave a Reply