2023: Atiku, Kwankwaso, Obi da Tinubu sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

2
264

‘Yan takara shugaban ƙasa na jam’iyyun siyasa 18 da za su fafata a zaɓen ranar asabar sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja.

Waɗanda suka halarci rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya akwai mambobin kwamitin zaman lafiya na ƙasa, da kuma shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Omoyele Sowore na jam’iyyar AAC da Bola Tinubu na jami’yar APC da Peter Obi na jam’iyyar LP da kuma Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP na daga cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa da suka halarci taron.

KU KUMA KARANTA: Zaɓen 2023: Matsayar kafafen yaɗa labarai na Arewa, daga Ɗan Agbese

2 COMMENTS

Leave a Reply