Yadda ‘yan bindiga sun kai farmaki makarantar firamare, suka yi awon gaba da ɗalibai

2
453

Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da ɗalibai 6 na makarantar firamare ta ƙaramar hukumar Alwaza da ke ƙaramar hukumar Doma a jihar Nasarawa su shida.

An ce ‘yan bindigar sun kai hari makarantar ne da misalin ƙarfe 7 na safiyar ranar Juma’a.

Rahman Nansel, mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar, ya tabbatar wa ‘yan jarida lamarin a ranar Juma’a.

Nansel ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike da ceto . “An tabbatar an sace ɗalibai shida.Sun mamaye makarantar da misalin karfe ƙarfe 7:10 na safe.

KU KUMA KARANTA:‘Yan bindiga sun nemi kuɗin fansa kan ɗaliban da suka sace a kai har Kogi

Ana ci gaba da bincike da ceto wanda Kwamishinan ‘yan sanda ya ke jagoranta yayin da ya gana tare da jajantawa iyayen waɗanda lamarin ya shafa,” in ji shi ta hanyar saƙon rubutu.

A halin yanzu dai jihar Nasarawa na ɗaya daga cikin jihohin arewa ta tsakiya da ke fama da matsalar rashin tsaro.

A tsawon shekaru ana kai hare-hare a kan al’ummar Nasarawa, wanda ya kai ga kashe-kashe, sace-sacen mutane, da kuma gudun hijira.

2 COMMENTS

Leave a Reply