Yau An Dakatar Da Zirga-zirga Don Ziyarar Buhari A Gusau

0
334

A ranar Alhamis ɗin nan ne Shugaba Muhammadu Buhari zai sauka a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, a wata ziyarar wuni guda da zai kai.

Tun a jajiberin ziyarar gwamnatin Zamfara ta bayar da sanarwar dakatar da zirga-zirgar ababen hawa ta tsawon sa’a uku a yayin ziyarar ta shugaban ƙasa.

Gwamnatin jihar dai ta ce ahugaban na Najeriya zai je Zamfara ne domin jajanta wa al’ummar jihar game da miyagun hare-haren ‘yan fashin daji na baya-bayan nan musamman a ƙananan hukumomin Anka da Bukkuyum.

Kwamishinan Yaɗa labarai na jihar Zamfara, Malam Ibrahim Magaji Dosara, ya shaida wa BBC cewa tuni suka kammala shirye-shiryen tarbar shugaban kasar.TALLAhttps://d6a25fa94d4efb40935cc0edaa385708.safeframe.googlesyndication.com/safeframe/1-0-38/html/container.html

Ya ce baya ga ta’aziyya da jajen da Shugaba Buhari zai yi wa al’ummar ta Zamfara, zai kuma kara wa sojoji Najeriya da ke jihar kwarin gwiwa a kan irin samame da sauran ayyukan da suke yi wajen fatattakar ‘yan bindigar da ke kai hare-hare a jihar da ma sauran jihohi.

Kwamishinan Yaɗa labaran ya ce daya daga cikin manufar ziyarar shugaban kasar a Zamfara ita ce domin ya sanyaya zukatan al’ummar ta Zamfara tare da nuna musu cewa yana tare da su.

Malam Ibrahim Dosara ya ce,” Ba jajen Anka da Bukkuyum kadai Shugaba Buhari zai yi ba, zai yi jaje ne ga dukkan iyalan wadanda suka rasa wani nasu a hare-haren ‘yan bindigar a jihar Zamfara”.

A cewarsa a yayin ziyarar shugaban kasar zai gana da jami’an tsaron da ke aiki a jihar da malamai da sarakunan gargajiya da kuma iyalan wadanda suka rasa ransu a yayin hare-haren.

Tuni dai gwamnatin jihar ta bukaci al’ummarta da su kiyaye da dukkan wasu dokoki a yayin ziyarar shugaban kasar.

Leave a Reply