A wajen bukin binne mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Tinubu ya yi kira da zaman lafiya da haɗin kan al’umma

0
196
A wajen bukin binne mahaifiyar shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Tinubu ya yi kira da zaman lafiya da haɗin kan al'umma
Shugaba Tinubu tare da Gwamnan Filato Mufwang

A wajen bukin binne mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Tinubu ya yi kira da zaman lafiya da haɗin kan al’umma

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga jama’ar Jihar Plateau da su zauna lafiya tare da haɗa kai don cigaban ƙasa da bunƙasar al’umma.

Tinubu ya yi wannan kira ne yayin da yake jawabi a wajen bikin jana’izar Nana Lydia Yilwatda a ranar Asabar a Jos.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa mamaciyar ita ce mahaifiyar Farfesa Nentawe Yilwatda, Shugaban Jam’iyyar All APC na ƙasa.

KU KUMA KARANTA: An kashe shanu 36, an ba wa 42 guba a Filato

Tinubu ya roƙi mazauna Plateau da ‘yan Najeriya gaba ɗaya da su guji bambancin addini da na ƙabila.

Ya ce, “Na gaji Musulunci daga iyalina, ban taɓa canzawa ba; amma matata fasto ce, kuma tana yi min addu’a koyaushe.

“Ban taɓa lallashinta ta canza addininta ba; ina amincewa da ‘yancin addini.

“Saboda haka, soyayyar da muke nuna wa juna ita ce abin da ya fi muhimmanci; dole ne mu koyi zama tare a matsayin jama’a ɗaya,” in ji shi.

Shi ma da yake jawabi, Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya gode wa shugaban ƙasa saboda ya samu lokaci duk da cunkoson ayyukansa domin halartar bikin jana’izar.

Leave a Reply