Hukumar Hisbah a Kano sun kama wanda ake zargi da safarar mata

0
110

Hukumar Hisbah a Kano sun kama wanda ake zargi da safarar mata

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta ce ta gano wasu Mata da ake zargin ana ƙoƙarin yin safararsu zuwa wasu ƙasashe domin neman kuɗi.

Mataimakin babban Kwamandan hukumar Dakta Mujahiddin Aminuddeen, ne ya bayyana hakan.

KU KUMA KARANTA: Mun karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776, mun warware rikicin aure 621 a shekarar 2024 – Hukumar Hisbah ta Kano 

Dakta Mujahiddin ya ce, hukumar ta ɗauki matakin gaggawa domin hana aukuwar lamarin tare da tabbatar da cewa, an tsare lafiyarsu, domin kariya daga fadawa cikin haɗarin cin zarafi ko bautar da su.

Leave a Reply