No menu items!

Sample Page Title

Date:

2027: Ba za mu tsayar da Atiku takara ba – PDP

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Bode George, ya ce dole ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya jira har zuwa 2031 idan ya na son ƙara yin takarar shugaban ƙasa.

Idan za a iya tunawa dai, Atiku yasha kaye a hannun shugaban ƙasa Tinubu a zaɓen shekarar 2023.

Mista George, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, ya ce dole ne ɗan kudancin ƙasar nan ya mulki Nijeriya daga 2023 zuwa 2031 inda ya ce “Saboda haka kundin tsarin mulkin PDP da zaman lafiyar mu ya nuna”.

“Duk da a 2027, zai cika shekaru 81, wannan ne lokacin da yakamata yayi koyi da shugaba Joe Biden ta hanyar baiwa matasa dama su yi takara.

” Bani da wani na kiyayya tsakani na da Alhaji Abubakar. Abokina ne amma dole ne a fadi gaskiya. Nan da 2027, idan Allah yaso zai kai shekaru 80.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Tinubu ba ta da alƙibila – Atiku

“To me nake nema, a kujerar shugabanci a yayin da na kai gargara? Irin hakan yakamata Atiku yayi.

” Dukkan mu munga yadda Joe biden ya janye takara tare da goyan bayan Kamala Harris a zaben shugaban kasa na watan Nuwamba a kasar.

“Wannan shi ne dattijantaka da Atiku yakamata yi irinta a 2027, PDP za ta tsayar da dan kudu ne takara a 2027”, inji George, tsohon Gwamnan soja na jihar Ondo.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...