2025: Mu haɗa kai mu ci gaba da tafiya domin gina ƙasar nan – Shugaba Tinubu

0
23
2025: Mu haɗa kai mu ci gaba da tafiya domin gina ƙasar nan - Shugaba Tinubu

2025: Mu haɗa kai mu ci gaba da tafiya domin gina ƙasar nan – Shugaba Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yi fatan alheri game da makomar Najeriya a shekarar 2025, inda ya ƙarfafa wa ’yan Najeriya gwiwa su ci gaba da kasancewa masu haɗin kai.

A cikin saƙon sabuwar shekarar da ya aike, Tinubu ya tabbatarwa da al’umma cewa sadaukarwarsu a watanni 19 da suka gabata ba za su tafi a banza ba.

“Da yardar Allah, shekarar 2025 za ta kasance shekarar cika alƙawari, inda za mu cika burinmu gaba ɗaya,” in ji Tinubu.

“Mu haɗa kai mu ci gaba da tafiya domin gina ƙasar nan.”

Shugaban ya yarda da matsalolin da ’yan Najeriya suka fuskanta a shekarar 2024, amma ya bayyana tabbacin cewa sabuwar shekarar za ta kawo canje-canje masu kyau.

Ya yi hasashen abubuwa kamar raguwar farashin man fetur, ƙara ƙarfin ajiyar ƙasa, da kuma haɓakar kasuwancin hannun jari.

Duk da haka, ya bayyana ƙarin farashin abinci da kayayyakin more rayuwa na ci gaba da zama babbar matsala a yanzu.

“Muna da niyyar rage hauhawar farashin kayayyaki daga kashi 34.6 zuwa kashi 15 kuma za mu yi ƙoƙari wajen rage tsadar rayuwa,” in ji shi.

KU KUMA KARANTA: Ina ƙira ga ;yan Najeriya a ƙara haƙuri da Tinubu ; Ganduje

Tinubu ya kuma bayyana shirin ƙirƙirar Kamfanin Kula da Lamuni na Ƙasa, wanda zai taimaka wajen bai wa ’yan kasuwa damar samun lamuni.
“Muna kan hanya daidaicciya wajen gina Najeriya mai ƙarfi,” in ji Tinubu.

Ya buƙaci ’yan Najeriya su mayar da hankali kan haɗin kai da aiki tare don gina ƙasa mai albarka.

Leave a Reply