Ɗaruruwan Falasɗinawa sun bijire wa hanin Isra’ila na shiga Masallacin Ƙudus a Juma’ar farko ta Ramadan

0
118

Duk da takunkumin da Isra’ila ta saka, dubban Falasɗinawa daga yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye sun samu damar shiga Masallacin Ƙudus da ke Gabashin Birnin Ƙudus a ranar Juma’a ta farko ta watan Ramadan, don gabatar da sallarsu ta mako-mako a cikin jam’i yayin da suke azumi.

“Musulmai kusan 80,000 ne suka yi Sallar Juma’a a Masallacin Ƙudus,” in ji Ma’aikatar Kula da Harkokin Musulunci a Birnin Ƙudus a cikin wata sanarwa.

Sheikh Ekrima Sabri, babban limamin Masallacin Ƙudus, ya yaba wa Falasɗinawa muminai kan shiga masallacin duk da takunkuman Isra’ila.

KU KUMA KARANTA: Saudiyya ta jaddada cewa ba za ta shirya da Isra’ila ba, sai ta tsagaita wuta a Gaza

“Kwarararku mai albarka tana isar da saƙo ga masu kwaɗayin shiga masallacin cewa ba ruwansa da rarrabuwar kawuna kuma na Musulmai ne kawai, babu inda za a yi sulhu ko a bar wani ɓangare nasa,” ya shaida wa masallatan.

Sabri ya buƙaci al’ummar Musulmi da su zo Masallacin Ƙudus, yana mai cewa, “Idan aka hana su, za su iya yin salla a inda ta riske su, tare da fatan samun ladan yin salla a Masallacin Ƙudus.

Leave a Reply