Ɗangote ya sake rage farashin litar man fetur
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Kamfanin matatar Ɗangote ya rage farashin man fetur zuwa ₦899.50k a kowace lita.
Wannan sanarwa ta fito ne cikin wata takarda da aka fitar da safiyar Alhamis.
Kamfanin ya bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne domin “bada sauƙi ga ‘yan Najeriya kafin lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.”
KU KUMA KARANTA: Matatar mai na Ɗangote ya rage farashin fetur ɗinsa
Matatar mai ta farko mai zaman kanta a nahiyar Afrika, wadda a baya ta rage farashin zuwa ₦970 a kowace lita a ranar 24 ga watan Nuwamba, yanzu ta sanar da sabon farashi na ₦899.50k a kowace lita.
“Wannan ragin farashin an yi shi ne da nufin rage kudin sufuri a lokacin bukukuwan karshen shekara,” in ji sanarwar da Babban Jami’in Yaɗa Labarai na Kamfanin, Anthony Chiejina, ya sa hannu.