Ɗangote ya rage farashin man fetur zuwa 820

0
265
Ɗangote ya rage farashin man fetur zuwa 820
Alhaji Aliko Ɗangote

Ɗangote ya rage farashin man fetur zuwa 820

Daga Shafaatu Dauda Kano

Kamfanin Man fetur na Dangote ya sanar da karin rangwamen farashin man fetur, inda sabon farashin ya koma Naira 820 a kowace lita daga Naira 840 da aka sayar a baya.

A cewar kamfanin, sabon farashin ya fara aiki daga jiya Talata, 8 ga Yuli, 2025.

Wannan sauyi na nufin ragin Naira 20 ne daga tsohon farashin man da kamfanin ke saidawa.

KU KUMA KARANTA: Matatar Ɗangote za ta rarrarba Man Fetur kai-tsaye zuwa gidajen Mai

Sabon matakin na zuwa ne kasa da mako guda bayan Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) ya rage farashin sayar da Mai daga Naira 945 zuwa Naira 910 a kowace lita.

Rangwamen na Dangote ya biyo bayan wani sauyin farashin da kamfanin ya yi makon da ya gabata, inda ya saukar da farashin daga Naira 880 zuwa Naira 840.

Leave a Reply