Ɗangote ya janye aniyarsa ta shiga kasuwancin sarrafa ƙarafa
Shugaban kamfanin Ɗangote, Alhaji Aliko Dangote ya sanar da janye aniyarsa ta shiga kasuwancin ƙarfe a Najeriya.
Janyewar da hamshaƙin ɗan kasuwar ya yi na zuwa ne watanni biyu bayan kamfaninsa ya sanar da cewa zai zuba jari a ɓangaren sarrafa ƙarafa domin faɗaɗa tattalin arziƙin Najeriya.
A yayin da yake jawabi ga manema labarai a Legas a ranar Asabar, shahararren mai kuɗin ya bayyana cewa kamfanin nasa ya janye daga wannan kasuwancin ne domin kada a zo ana zargin kamfaninsa da babakere.
Fitaccen ɗan kasuwar ya kuma yi watsi da zargin da ake yi wa wasu kamfanoninsa na babakere a harkokin kasuwanci.
“Kun san kan batun sabon kasuwancin da muka sanar, wanda shi ne na ƙarafa, a gaskiya kamfaninmu ya yanke shawarar cewa ba za mu yi kasuwancin ƙarfe ba domin idan muka yi kasuwancin, za a rinƙa ƙiranmu da sunaye iri-iri kamar masu babakere,” in ji shi.
KU KUMA KARANTA: Matatar Ɗangote na zargin manyan kamfanonin mai na duniya da hana shi samun ɗanyen fetur
“Haka kuma za a bayar da ƙwarin gwiwar shigo da kayayyaki, ba za mu so mu shiga nan ba.”
“Idan kuka dubi duka ayyukanmu a Ɗangote (Group), muna ƙara ƙima; mukan dauki kayayyaki wanda aka samar da su a cikin ƙasa mu sarrafa su zuwa kayayyakin amfani, mu kuma sayar.
Ba mu taba hana kowa a sane ko cikin rashin sani ba daga yin irin kasuwancin da muke yi. “Lokacin da muka fara kasuwancin siminti, Lafarge ne kawai ke aiki a nan Najeriya.
Babu wanda ya taba ƙiran Lafarge a matsayin mai babakere,” in ji shi. Shugaban kamfanin na Ɗangote ya bayyana cewa ƙiran kamfaninsa da ake yi da mai babakere ba ya yi masa daɗi a ransa.