Ɗangote ya ba da tallafin karatu ga al’ummar da ya gina kamfani a yankinsu

Ɗangote Granite Mines, reshen rukunin Ɗangote, ya ba da tallafin karatu ga ɗalibai kusan 60 a cikin ƙauyuka biyar, waɗanda Ɗangote ya gina kamfani a yankinsu.

Kamfanin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da Francis Awowole-Browne ya fitar a Legas ranar Lahadi.

Mista Awowole-Browne ya bayyana cewa tallafin na wani ɓangare ne na Hukumar Kula da Jama’a ta Kamfanin, CSR, don bunƙasa ilimi a cikin al’ummomin da ke aka gina kamfanin a yankin.

Ya yi nuni da cewa, Ebenezer Ali, daraktan kula da kadarorin jama’a na ayyukan Ɗangote, ya ce an bayar da tallafin ne domin a taimaka wa iyayen waɗanda suka amfana, da su rage musu nauyin karatun ‘ya’yansu.

KU KUMA KARANTA: A bawa ɗalibai tallafin karatu, ba bashin kuɗin karatu ba – ƙiran ASUU ga gwamnatin tarayya

Malam Ali ya ƙara da cewa tallafin na daga cikin yarjejeniyoyin da aka cimma da shugabannin al’ummomin da suka karɓi baƙuncinsu a lokacin da aka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar ci gaban al’umma (CDA).

Ya ce an ɗauki matakin ne domin tabbatar da cewa ba a bar al’ummomin da suka ba wa Ɗangote damar gina kamfani a yankin, a baya ba a fannin ilimi da ci gaban ababen more rayuwa.

Ali ya buƙaci waɗanda suka ci gajiyar shirin da su fuskanci karatunsu domin za a ba su aikin yi a take idan sun yi ƙoƙari a fannin ilimi.

Ya godewa shugabannin al’umma bisa samar da yanayi na zaman lafiya a yankin da kuma nuna fahimtar juna da ta kai ga samun kwanciyar hankali da kamfani da al’umma ke samu.

Ya kuma tabbatar wa al’umma shirin kamfanin na yin nasu ɓangaren na yarjejeniyar wajen tabbatar da sun haɗa da mutanen a kowane lokaci.

“Ina ƙira ga shugabannin al’umma da su ci gaba da tallafawa harkokin ma’adinan Ɗangote Granite ta hanyar wanzar da zaman lafiya,” in ji shi.

Wani Sarkin Ijebu Igbo, Sopenlukale na Oke Sopen, Oba Adesesan Yussuf, ya godewa mahukuntan rukunin Dangote bisa taimakon da suke baiwa al’umma.

Sarkin ya ce tallafin ya nuna cewa kamfanin ya kasance mai son jama’a kuma ya jajirce wajen bayar da gudummawa ga al’umma don haka ya cancanci duk wani tallafi da al’umma za su iya samu.

Ya shawarci ’yan uwa da su ci gaba da wanzar da zaman lafiya, inda ya ce sai an samu zaman lafiya ne kamfanin zai iya taimakawa al’umma da kyau.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka ci gajiyar tallafin, Grace Aregbe na Jami’ar Ilimi ta Tai Solarin, (TASUED), ta godewa kamfanin bisa wannan karamcin.

Ta ce tallafin zai taimaka matuƙa wajen rage wahalhalun da za su fuskanta a makaranta.

Ta yi alƙawarin cewa waɗanda suka ci gajiyar shirin ba za su ƙyale kamfanin da iyayensu ba, sannan ta yi addu’ar Allah ya ba shugaban kamfanin Aliko Ɗangote lafiya.


Comments

One response to “Ɗangote ya ba da tallafin karatu ga al’ummar da ya gina kamfani a yankinsu”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Ɗangote ya ba da tallafin karatu ga al’ummar da ya gina kamfani a yankinsu […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *