Ɗan kasuwa ya nemi kashe matarsa don ya ƙara jari a shagonsa

0
160

An cafke wani ɗan kasuwa kan yunƙurin kashe matarsa don ya samu damar sayar da talabijin ɗinsu ya ƙara jari a shagonsa a Jihar Bauchi.

Magidancin mai shekaru 35 ya shiga hannu ne bayan ya yi amfani da taɓarya wajen dukan matar tasa da nufin kashe ta.

Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta ce, magidancin, ya shaida wa masu bincike “cewa ya yi niyyar kashe matarsa ne don ya ɗauki talbijin ɗinsu ya sayar, ya samu kuɗi ya ƙara kaya a shagonsa.”

Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya ce an kai matar asibitin ƙwararru da ke Bauchi domin kulawar da ita a sakamakon munanan raunukan da mijin ya yi mata da taɓarya.

KU KUMA KARANTA: Mugun mafarki ya ingiza matashi buga wa mahaifinsa taɓarya a Kaduna

“Bincike na farko ya nuna wanda ake zargin ya amsa tuhumar da ake masa ba tare da wata turjiya ba.

“Ya yi iƙirarin cewar ya yi ƙaryar cewa ’yan fashi sun shiga gidansu, shi ne ya shiga ɗakin da suke kwance da matarsa ​​ya ce mata ta rufe kanta da gyale.

“Sai ya fita ya je ya rufe fuskarsa da mayafi, sannan ya ɗauko taɓarya ya dawo ɗakin ya fara dukanta da ita,” in ji kakajin rundunar.

Ya ce abin ya faru ne a ranar Asabar, 2 ga watan Disamba, 2023, kuma kwamishinan ’yan sandan jihar, Auwal Mohammed, ya bayar da umarnin miƙa wanda ake zargin ga sashen binciken manyan laifuka don zurfafa bincike da kuma gurfanarwa a kotu da zaran an kammala bincike.

Leave a Reply