Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wani matashi ɗan shekara 24 mai suna Amos Christopher bisa zarginsa da lakaɗa wa ƙaninsa duka ya mutu har Lahira.
Wanda ake zargin wanda aka ce yana fama da ciwon farfaɗiya, ana zargin ya kashe ɗan su na ƙarshe, Thyson Christopher mai shekaru 4, daga bisani kuma ya fille kansa a ranar Litinin, 19 ga watan Yuni.
A cewar rundunar ‘yan sandan, wanda ake zargin wanda shi ne na farko a gidansu, ya yanke jiki ya faɗi a ranar 18 ga watan Yuni, inda maƙwabta suka ɗauko shi suka dawo da shi gida.
An ba da rahoton cewa yanayin lafiyarsa ya taɓarɓare tare da sauya halayensa da safe ya far wa mahaifiyarsa da ƙannensa da ke gida tare da shi da ƙarfi.
KU KUMA KARANTA: Wasu ‘yan bindiga sun kashe ma’aikacin INEC, sun sace matarsa a Ebonyi
An ruwaito cewa ya kama yaron ɗan shekara 4 ya ja shi zuwa cikin ɗaki inda ya kulle kofar ya yi masa duka ya mutu har Lahira.
Duk ƙoƙarin ceto yaron da mahaifiyarsa ta yi ya ci tura. A halin da yake ciki na tashin hankali, an yi zargin ya kai gawar waje inda ya yi amfani da fartanya da ke hannunsa wajen datse kan yaron tare da fasa kan gida biyu.
A yayin da Kakakin Rundunar SP Suleiman Yahaya Nguroje ke yi masa tambayoyi, wanda ake zargin da ƙyar ya yi magana ya ce bai yi komai ba, kuma ƙanin nasa yana gida.
Da yake amsa tambayoyi, mahaifin waɗanda ake zargi da kuma wanda aka kashe, Christopher Haruna, ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da yake gona, ya kuma tabbatar da cewa Amos na fama da farfaɗiya.
[…] KU KUMA KARANTA: Ɗan fari ya kashe ɗan autansu da duka, ya raba kansa gida biyu […]