Connect with us

Labarai

Ɗage haramcin shigo da shinkafa Najeriya barazana ce garemu — In ji manoma

Published

on

Ƙungiyar masu sarrafa shinkafa ta Nijeriya, wato RIMAN, ta bayyana damuwa game da matakin gwamnatin ƙasar na ɗage haramcin shigar da wasu kayayyaki daga ƙasashen waje ciki har da shinkafa.

Shinkafa na cikin kayayyakin da gwamnatin Najeriya ta haramta shigar da su a shekarar 2015 cikin ƙasar a wani mataki na ƙoƙarin bunƙasa noma a ƙasar da nufin dogaro da kai.

Ƙungiyar masu sarrafa shinkafar ta cikin gida, ta ce matakin ɗage haramcin babbar barazana ce bayan sun zuba maƙudan kuɗi a kasuwancin.

Shugaban ƙungiyar, Peter Dama, ya shaida wa BBC cewa, a gaskiya wannan mataki ya zame musu kamar bala’i ne domin gwamnati ta sanya sun sanya kuɗaɗensu sun sayi kayan sarrafa shinkafa, sannan an sa jama’a sun shiga noma shinkafar, ga shi jama’ar ƙasa sun fara son shinkafar da ake samarwa a gida, “sai kawai mu ji an ce an ɗage haramcin shigo da shinkafar waje.”

KU KUMA KARANTA: An ba da umarnin buɗe iyakokin Najeriya, don a shigo da kayan abinci da sauran kayayyaki

Ya ce, “ Wannan mataki na gwamnati ya kawo mana cikas, ga shi kuma zai sa a rufe kamfanoni da dama, sannan jama’a da yawa za su rasa aikin yi ga shi kuma manoma da dama kuma ba za su yi aikin shinkafa, kuma sannan za a fara shigo mana da shinkafar da ta riga ta ruɓe.”

Peter Dama, ya ce: ‘’Gwamnati ba ta shawarce mu ba kafin ta ɗauki wannan mataki, kuma batun cewa shinkafar da ake samarwa a gida ma tana tsada ai kowa ya san ba da ruwa ake nomata ba, kuma yadda ake noman nata ma ai sai a duba a gani, sannan wajen ban ruwa ba wasu da ƙananan inji suke yi kuma ai da man fetur ake amfani a injin, kuma kowa ya san tsadar mai a yanzu.”

Shugaban ya ce babbar damuwarsu idan har aka fara shigar da shinkafar waje to mutane sai su koma kanta domin su al’ummar Najeriya idan aka ce musu ga wani abu na waje ko da ruwan sha ne sai hankalinsu ya koma kansa.

Ya ce, “ Mu mun yi iya bakin ƙoƙarin mu wajen nunawa ‘yan Najeriya cewa shinkafarmu ta gida ta fi auki sannan ta fi amfani a jiki domin mu ta mu ba a ajiye ta ta yi shekara da shekaru ba.”

“Mu ba ma yi wa shinkafarmu ta gida doguwar ajiya.”

Ya ce, “A yanzu mu matakin da za mu ɗauka shi ne za mu yi magana da gwamnati mu ba ta shawara, sannan mu saurara mu ji ko za su saurari kokenmu.”

Peter Dama, ya ce,” Idan har ana so a samu sauƙin tsadar shinkafa a ƙasa to sai a rage kuɗin man fetur da na kayan aikin gona, da kuma ba wa manoma taimakon da zai bunƙasa nomansu.”

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like