Connect with us

Ƙasashen Waje

Ƴan gudun hijirar Sudan da ke Chadi na fuskantar tsananin rayuwa shekara guda da soma yaƙi

Published

on

Shekara ɗaya bayan ɓarkewar yaƙi Sudan, Alabaki Abbas Ishag mai shekara 24, yana rayuwa a sansanin ƴan gudun hijira da ke Chadi da ke makwabtaka.

Ishag yana cikin mutum miliyan 8.5 da yaƙin da ke gwabzawa tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF ya raba da muhallansu.

Ya isa ƙauyen Koufroun na Chadi da ke kan iyaka bayan ya kwashe shekara ɗaya yana ɓuya — da zummar tsere wa hare-haren da ake kai wa a yankin Darfur da ke yammacin ƙasar.

Ya yi ta ɓuya a cikin gine-gine da aka lalata a yankin El-Geneina, babban birnin Yammacin Darfur.

Yaƙi ya ɓarke ne ranar 15 ga watan Afrilu tsakanin sojojin Sudan ƙarƙashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan da dakarun kai ɗaukin gaggawa na Rapid Support Forces (RSF) da ke ƙarƙashin tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo.

A El-Geneina kaɗai, an kashe tsakanin mutum 10,000 zuwa 15,000 a watanni tara a farkon yaƙin, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Rundunar RSF “ta yi yunƙurin ɗauka ta a matsayin soja domin na taya ta kai hare-hare, amma bayan da na ƙi bin umarninta sai ta sanya ni a cikin jerin mutanen da za ta kashe”, in ji Ishag.

“Ina kallo suna jefa mutanen da na sani a cikin manyan ƙaburbura suna binne su da ransu.”

KU KUMA KARANTA: Ana zargin tsohon firaiministan Sudan Hamdok da laifin ‘tunzura’ mutane su yi yaƙi

Ishaq ya isa garin Koufroun, inda ya yi saye da sayawar don samun na kashewa. Hakan ya ba shi damar cin abinci aƙalla sau ɗaya a kowace rana.

Sai dai yana cike da fargaba sakamakon matsowar damuna.

Yanzu ƴan gudun hijirar Sudan kimanin miliyan ɗaya suna zaune a Chadi — ita ce ƙasar da ta fi yawan ƴan gudun hijirar Sudan.

A cikin shekara ɗaya da ta wuce, ƴan gudun hijirar Sudan sama da 571,000 suka je Chadi ta ƙasa, ƙari a kan fiye da mutum 400,000 da suka shigar ƙasar sakamakon yaƙin da aka yi a Darfur a 2003.

Ƴan gudun hijira sama da 160,000 suke tsugune a sansanin Adre da ke kan iyala, wanda shi ne wuri na farko da mutum zai isa idan ya tsallaka iyaka.

Hada Ishag Fadallah ta isa Adre tare da ƴayanta bakwai a farkon watan Nuwamba.

“Dakarun RSF sun zo gidanmu inda suka harbe mijina sannan suka sace duk abin da muka mallaka, kuma wasu daga cikinsu sun doke mu,” a cewar Ishag, mai shekara 56.

Mata da ƙananan yara su ne kusan kashi 90 na ƴan gudun hijirar Sudan da suka isa Chadi a cikin shekara ɗaya da ta gabata, in ji MDD.

A watan da ya gabata, Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ta yi gargaɗi cewa za ta dakatar da tallafin abinci ga ƴan gudun hijirar Sudan da ke Chadi a watan Afrilu saboda ƙarancin kuɗi, inda ta yi kira a ba ta taimakon ƙarin kuɗaɗe domin kauce wa faɗawa cikin “babban bala’i”.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

Harin ta’addanci ya kashe sama da mutane 20 a Mali

Published

on

Harin ta'addanci ya kashe sama da mutane 20 a Mali

Harin ta’addanci ya kashe sama da mutane 20 a Mali

Wani hari da ake kyautata zaton masu ikirarin jihadi ne suka kai ƙauyen Djiguibombo da ke kusa da garin Bandiagara a yankin tsakiyar ƙasar Mali, ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 20, kamar yadda wasu hukumomin yankin biyu suka tabbatar.

Majiyoyin da suka nemi a sakaya sunansu sun tabbatar da mutuwar mutane 20, sannan suka ce yadda lamuran tsaro suka taɓarɓare a yankin, ya hana jami’an tsaro kai ɗauki wajen.

Wani jagoran matasan yankin shi ma da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tun a farkon daren ranar Litinin ɗin data gabata ne maharan suka kai farmakin, inda suka kwashe tsawon sa’oi uku a cikin garin.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe ‘yan jarida 106 a yakin da take yi a Gaza — Jami’ai

Ya ce sama da mutane 20 ne aka kashe a harin, kuma fiye da rabinsu matasa ne inda aka ranke musu harsuna.

Kasar Mali dai na fama da matsalolin tsaro na ƙungiyar Al-Qaeda da kuma na IS tun a shekarar 2012, inda ya bazu kasashen Burkina Faso da Nijar da ke makwabtaka da ita.

Tun bayan ƙwace mulki da sojoji suka yi a kasar a shekarar 2020, hukumomi  ke jin tsoron fitowa fili su sanar da labarin hare-haren ta’addancin da ake kai wa kasar da ke Yammacin Afrika.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

A shirye muke mu yaƙi Hizbollah idan har ta kama – Ministan Tsaron Isra’ila

Published

on

A shirye muke mu yaƙi Hizbollah idan har ta kama - Ministan Tsaron Isra'ila

A shirye muke mu yaƙi Hizbollah idan har ta kama – Ministan Tsaron Isra’ila

Ministan Tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya ce sojojin Isra’ila za su kasance a shirye don daukar duk wani matakin da ya dace kan ƙungiyar Hizbullah ta ƙasar Labanon, ko da yake abin da ake so shi ne cimma matsaya ta shawarwari.

Muna kai wa ƙungiyar Hizbullah hari sosai a kowace rana kuma za mu kai ga cikakken shiri na ɗaukar duk wani mataki da ake buƙata a ƙasar Labanon, ko kuma cimma wani shiri daga matsayi mai ƙarfi.

KU KUMA KARANTA: Gaza ya zama gidan marayu kuma maƙabartar yara mafi girma a duniya – Emine Erdogan

Mun fi son tsari, amma idan aka kai mu maƙura za mu san yadda za mu yi yaƙi,” an ruwaito Gallant a wata sanarwa da ofishinsa ya fitar.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Mutum 12 ne suka mutu, 20 suka jikkata a wani hari da aka kai wata kasuwa a Yammacin Sudan

Published

on

Mutum 12 ne suka mutu, 20 suka jikkata a wani hari da aka kai wata kasuwa a Yammacin Sudan

Mutum 12 ne suka mutu, 20 suka jikkata a wani hari da aka kai wata kasuwa a Yammacin Sudan

Aƙalla mutum 12 ne suka mutu yayin da wasu 20 suka jikkata a jiya Laraba a wani hari da aka kai kan wata kasuwar dabbobi da ke El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa a Yammacin Sudan.

A wata sanarwa da kwamitin sulhu na kwamitocin ‘yan gwagwarmaya na El Fasher ya fitar ya ce “harbin bindigogi a kasuwar dabbobi da ke birnin El Fasher ya yi sanadin mutuwar fararen hula 12 da kuma wasu 20 da suka samu raunuka daban-daban.”

Tun da fari a ranar Larabar da safe, kwamitocin ‘yan gwagwarmaya sun ce dakarun Rapid Support Forces (RSF) sun kai mummunan hari El Fasher da manyan bindigogi.

Tun a ranar 10 ga Mayu, aka fara ƙazamin fada tsakanin sojojin Sudan da RSF a El Fasher. Majalisar Dinkin Duniya da ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa ke amfani da birnin a matsayin cibiyar ayyukan jinƙai ga yankin Darfur.

Rikicin Sudan ya ɓarke ne a cikin watan Afrilun 2023 tsakanin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kwamandan RSF Mohamed Hamdan Dagalo kan yarjejeniyar shigar da RSF cikin rundunar soja.

KU KUMA KARANTA: Adadin mutanen da suka rasa muhalli a sassan duniya ya zarta miliyan 114 — MƊD

Ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 16,000, da raba kusan mutum miliyan 10 da muhallansu, sannan sama da miliyan 25 na buƙatar agajin jinƙai, lamarin da ya zama mafi girma a duniya ta ɓangaren matsalar rashin matsuguni da yunwa, a cewar MƊD.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like