Ƙungiyoyin ma’akatan jihar Yobe sun sha alwashin inganta ayyukansu

Daga Sa’adatu Maina, Damaturu

Shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Yobe a tsakanin Daraktoci da Shugaban Ma’aikatun sun gudanar da taron kwana guda a jihar domin inganta ayyukan ma’aikata wajen samar da ayyuka.

Taron ya gudana ne a ɗakin taro na ƙaramar hukumar Damaturu, inda shugaban ma’aikata na jiha Alhaji Garba Bilal ya ce ma’aikatan gwamnati ita ce babbar hanyar da gwamnati ke aiwatarwa da gudanar da manufofi da tsare-tsare.

Bilal ya bayyana cewa, su ma ma’aikatan gwamnati suna da rawar da za su taka wajen bayar da hidima inda ya ƙara da cewa babu yadda za a yi ma’aikatan za su ci gaba da tafiya ba tare da gudunmawarsu ta wata hanya ba.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin jihar Yobe ta fara aikin tituna da magudanan ruwa

“Taron na mutane ne masu mahimmanci, a matsayin Daraktoci, Shugaban Ma’aikatun su ne mutanen da ke da alhakin kula da duk wasu muhimman takardu na gwamnati.

“A matsayinku na Daraktoci a ma’aikatu da shugaban hukumomi a MDAs daban-daban, kuna da rawar da za ku taka wajen ciyar da ma’aikatan gwamnati gaba,” inji Bilal.

Ya bayyana cewa, ci gaban da aka samu a ƙasashen duniya da dama ya samo asali ne sakamakon yadda ma’aikatansu suke da fasaha wajen fassara manufofin shugabannin siyasarsu yadda ya kamata zuwa ayyuka na zahiri.

Don haka Alhaji Garba Bilal ya yi ƙira ga manyan ma’aikatan jihar a wajen taron da su sanya hannu a kan teburi don bayar da gudunmawa mai tsoka domin ciyar da jihar gaba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *