Ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa, ta je ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar mawallafin jaridar Neptune Prime

0
184

Daga Ibraheem El-Tafsser

Ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa reshen jihar Yobe, sun je ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar Dakta Hassan Gimba (mawallafin jaridar Neptune Prime) a gidansu da ke garin Potiskum jihar Yobe. Ziyarar ta gudana ne ƙarƙashin jagorancin shugaban ‘yan jaridar na jihar Yobe, Alhaji Rajab Mohammed.

Ziyarar sun wakilci dukkan ‘yan jaridar jihar Yobe da ma na ƙasa baki ɗaya, domin yi masa ta’aziyya na wannan babban rashi.

Rajab ya bayyana rashin Hajiya Hafsat a matsayin babban giɓi wadda zai wahala a maye gurbinsa. “rashin Hajiya babban rashi ne ga dukkanmu ba ga iya ‘ya’yanta kawai ba. Muna addu’ar Allah ya jiƙanta da rahama”.

KU KUMA KARANTA: Masarautar Fika, Pataskum da Tikau sun je ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar mawallafin jaridar Neptune Prime

Daga cikin waɗanda suka masa rakiya, akwai mataimakin shugaban ‘yan jaridar na jihar Yobe, Usman Nasoro, Sakatare, Alhassan Sule Mamuɗo, Treasurer, Baba Shehu Mohammed da Auditor, Murjanatu Yelwa.

Leave a Reply