Ƙungiyar ‘yan jarida a Yobe sun gana da shugaban majalisar jihar

1
358

Daga Ibraheem El-Tafseer

Shugaban ƙungiyar ‘yan Jarida (NUJ) na jihar Yobe Kwamared Rajab Mohammed Ismail ya jagoranci kwamitin wasannin NUJ Media na 2023 a ziyarar ban girma ga shugabannin majalisar dokokin jihar Yobe.

Kwamared Rajab a lokacin da yake taya sabon shugaban majalisar da shugabannin majalisar murna ya sanar da shi game da wasannin NUJ Media na 2023 da ke tafe inda ya miƙa wa kakakin majalisar takardar gayyata wasannin da aka shirya za su fito a ranar Asabar 29 ga Yuli, 2023 a cibiyar ‘yan jarida ta NUJ dake Damaturu.

KU KUMA KARANTA: Ranar ‘yan jarida ta ƙasa: Za mu bada goyon baya wajen yaɗa sahihancin labarai da kare ‘yancin ‘yan jarida – Kwamared Rajab

A nasa martanin shugaban majalisar Chiroma Buba Mashio, ya ce sabuwar manufarsa ta buɗe kofa ce tare da bayyana aniyarsa ta marawa ƙungiyar NUJ baya ta fuskar kawo tsare-tsare na samar da zaman lafiya da shugabanci na gari a jihar.

Taron ya samu halartar manyan jami’an majalisar da wasu ‘yan majalisar jihar.

1 COMMENT

Leave a Reply