Ƙungiyar ‘Women Connect Movement’ ta yabawa Kashim Musa Tumsa (KMT)

0
369
Ƙungiyar 'Women Connect Movement' ta yabawa Kashim Musa Tumsa (KMT)

Ƙungiyar ‘Women Connect Movement’ ta yabawa Kashim Musa Tumsa (KMT)

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙungiyar Mata mai suna ‘Women Connect Movement’ ta shiyyar Yobe ta Kudu (Zone ‘B’) ta yabawa Kashim Musa Tumsa (KMT) bisa la’akari da irin ayyukan da ya ke yi waɗanda suka shafi al’umma kaitsaye, ƙoƙarin tallafawa al’umma, jagoranci mai haɗa kai, da jajircewarsa na ƙarfafa mata a faɗin jihar Yobe. Shugabar ƙungiyar, Hajiya Amina Ibrahim, ce ta yi wannan jinjinar a yayin wani taro da aka faɗaɗa a Potiskum, da nufin ƙarfafa goyon bayan KMT da ke tasowa.

A yayin taron, shugabar mata ta shiyyar Zone ‘B’ Women Connect, ta yaba da irin tsare-tsare da da KMT ke yi na sake gina amanar jama’a da kuma dawo da ƙwarin gwiwar gudanar da mulkin jihar Yobe. Ta kuma jaddada cewa shugabancinsa ya sake haifar da sabon fata da a tsakanin al’umma.

KU KUMA KARANTA:An ƙaddamar da buɗe gadar da KMT ya gina a Rugar Fulani Potiskum (Hotuna)

“Mun yi sa’a don samun ɗan’uwa mai saurare kuma abokinmu jagora mai sadaukarwa kuma uba ga kowa, ba tare da la’akari da siyasa ko ƙabila ba,” in ji ta. “Idan aka dubi kyawawan abubuwan da ke faruwa a jihar Yobe cikin watanni biyun da suka gabata, a bayyane yake cewa muna shiga wani sabon zamani na fata da ci gaba.”

Rahotanni daga dukkan ƙananan hukumomin 17 sun nuna matuƙar gamsuwa. Jama’a a faɗin jihar suna nuna matuƙar godiya ga jagoranci mai tasiri da hangen nesa na KMT.

Leave a Reply