Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta yi Allah wadai da harin Isra’ila a Rafah

0
50

Ƙungiyar Tarayyar Afrika AU ta yi Allah wadai da shigar sojojin Isra’ila kudancin Rafah a zirin Gaza, tana kira ga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa su tsayar da “wannan mummunan yaƙi da ya ƙi ci – ya ƙi canyewa.”

Shugaban na AU Moussa Faki Mahamat “ya yi kakkausar suka kan yadda yaƙin ya tsallaka zuwa mashigar Rafah”, a cewar wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Laraba, bayan Isra’ila ta ƙwace iko da muhimmiyar hanyar da ake da ita wajen shigar da agaji zuwa yankin Falasdinawa da aka mamaye.

Faki “ya nuna matuƙar damuwa kan yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza, wanda a ko da yaushe yake janyo asarar rayuka da tarwatsa yanayin rayuwar jama’a,” a cewar sanarwar.

KU KUMA KARANTA: Kwamitin Tuntuɓa kan Gaza, da Turkiyya sun tattauna kan zamowar Falasɗinu ƙasa mai ‘yanci

“Ya yi kira ga duniya baki ɗaya ta tsara ɗaukar wani mataki na tsayar da mummunan yaƙin.”

Kutsen da Isra’ila ta yi Rafah, wajen da ke maƙare da fararen hular da aka tilastawa barin gidajensum na zuwa ne a lokacin da masu sasantawa da masu shiga tsakani ke ganawa a Masar domin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da aka shafe wata bakwai ana yi.

A ranar Laraba Isra’ila ta ce ta sake buɗe iyakar Kerem Shalom don shigar da agaji Gaza, kwana huɗu bayan rufe ta, a matsayin martani kan harba makaman roka da suka janyo mutuwar sojojin Isra’ila huɗu.

Ta ce a karon farko tun fara yaƙin, an buɗe iyakar Erez tsakanin Isra’ila da arewacin Gaza don shigar da agaji yankin na Falasɗinawa.

Majalisar Ɗinkin Duniya da Amurka babbar ƙawar isra’ila sun yi Allah wadai da rufe iyakokin, waɗanda su ne hanyoyin da fararen hula ke samun abin da za su ci su rayu, a daidai lokacin da ake fuskantar tsananin yunwa a yankin

Leave a Reply