Ƙungiyar Shi’a Rasulul-A’azam Foundation ta nemi a saka ta cikin kwamitin shura ta Kano
Daga Idris Umar Zariya
A ci gaba da cece-kuce da ke gudana a jihar Kano dangane da zargin yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW), ƙungiyar Shi’a ta Rasulul-A’azam Foundation reshen jihar Kano ta nemi gwamnatin jihar Kano da ta sanya wakilanta cikin Kwamitin Shura da ke duba batun muƙabala da Malam Lawal Triumph.
Shugaban ɓangaren da’awa na ƙungiyar, Sheikh Lawal Bashir, ne ya jagoranci tawagar zuwa ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruq Ibrahim, domin miƙa koke da buƙatar su.
KU KUMA KARANTA: Dalilin da ya sa ‘yansandan Kano suka gayyaci Sheikh Lawan Triumph
Sheikh Lawal ya bayyana cewa, a matsayinsu na ‘yan ƙasa masu bin doka kuma kungiya mai rijista, ya kamata gwamnati ta riƙa bai wa kungiyar dama a harkokin gudanarwa da na shari’a, musamman ma a lokutan da ake buƙatar hadin kai da zaman lafiya a cikin al’umma.
Ya nuna damuwarsu kan yadda aka takaita wakilcin kwamitin Shura ga kungiyoyi kamar Izala da Ɗariƙa Tijjaniyya kawai, yana mai cewa:
Ya kamata a rinka Sanyasu cikin al’amuran Gwamnatin don suma sunada rawar da zasu taka a matsayin su yan kasa masu iko kuma musulmi.

Malamin ya kuma jaddada cewa kungiyarsu ta taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar wannan gwamnatin mai ci yanzu don haka bai dace a ware su ba a irin wannan lokaci mai sarkakiya.
Ya yi gargadi ga gwamnatin Kano da kada ta maimaita kuskuren da gwamnatin da ta gabata ta yi, wanda a cewarsa shi ne ya janyo wasu daga cikin matsalolin rashin girmamawa ga Annabitt Muhammad (SAW) da ake fuskanta yanzu.
Kuma yayi fatan za a tabbatar da adalci a lamarin don yin adalci shike kawo zaman lafiya a cikin al’ummar ƙasa.
A karshe, Sheikh Bashir ya bayyana cewa Sakataren Gwamnatin jihar, Alhaji Faruq Ibrahim, ya karɓi korafinsu tare da yi musu alkawarin duba batun da niyyar ɗaukar matakin da ya dace, da taimakon Allah.









