Ƙungiyar kare ‘yancin Musulmi ta MURIC, ta soki kwamitin da gwamnatin Filato ta naɗa don warware rikicin Mangu

0
133

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙungiyar kare ‘yancin Musulmi a Najeriya (MURIC) ta zargi gwamnanatin jihar Filato da nuna wariya da ƙyama ga al’ummar Musulmi saboda rashin sanya musulmi ko ɗaya a cikin kwamitinta na tsaro da ta haɗa mai mutum 11 domin warware rikicin ƙabilanci a garin Mangu da kewaye.

A ranar Laraba ne dai gwamnan jihar Filato, Caleb Manasseh Mutfwang ya naɗa kwamitin na tsaro na mutum goma sha ɗaya domin nemo bakin zare dangane da yadda rikicin ƙabilanci ya dabaibaye al’ummar a ‘yan watannin nan.

Shugaban ƙungiyar ta MURIC, Farfesa Ishaq Akintola a wata sanarwa ga manema labarai “akwai alamar tambaya a ce kwamiti mai mutum 11 amma babu sunan Musulmi ko ɗaya alhali kuma a cikin ƙabilun da ake rikicin da su a kwai Musulmi. Wannan ya nuna cewa da wuya a yi adalci.”

KU KUMA KARANTA: An samu arangama tsakanin sojoji da wasu mutane a Mangu da ke Filato

Sai dai gwamnatin jihar Filato ta ce mutane ba su fahimci ainihin aikin komitin ba ne, inda ta musanta zargin nuna wariyar da ake yi mata.

Leave a Reply