Ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin harin da ya yi ajalin fiye da mutum 80 a Iran

0
150

Ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin ƙaddamar da harin tagwayen bama-bamai da ya kashe fiye da mutum 80 a wurin taron tunawa da babban kwamandan sojin Iran, Qassem Soleimani wanda jirgin Amurka mara matuki ya kashe shi a Iraqi a shekarar 2020.

IS ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da wallafa a shafin Telegram.

A cewar ƙungiyar, mayaƙanta ne suka tayar da bama-baman da suka yi ɗamara da su a cikin dandazon jama’ar da suka hallara a maƙabartar da aka binne Soleimani da ke birnin Kerman a ranar Laraba.

Bayanai sun ce tagwayen hare-haren sun kuma raunata mutane 284 da suka haɗa da mata da ƙananan yara.

Za mu yi zazzafar ramuwa kan waɗanda suka kai harin ta hanyar amfani da sojojin Soleimani, inji Mohammad Mokhber, mataimaki na farko na shugaban ƙasar Iran.

Tun da farko, wata majiya ta shaida wa Kamfanin Dillacin Labaran Gwamnatin Ƙasar Iran cewa, wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bam ɗin farko a wurin taron tunawa da Soleimani wanda aka kashe shekaru huɗu da suka gabata.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kai hari a ofishin ƙungiyar Palestinian Red Crescent

Majiyar ta ce, ga alama shi ma bam na biyu ya tashi ne bayan wani ɗan ƙunar baƙin waken ya sake tayar da shi.

Tuni Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi tur da wanna harin da ya bayyana a matsayin na matsoratan ’yan ta’adda a Kerman, yana mai miƙa sakon ta’aziyarsa ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su da kuma gwamnatin ƙasar.

Kafar talabiji ta ƙasar ta nuna hotunan dandazon Iraniyawa a sassan biranen ƙasar suna rera wake-waken, inda suke cewa “mutuwa ta tabbata ga Isra’ila”. “Mutuwa ta tabbata ga Amurka.”

Hukumomin Iran sun buƙaci gudanar da gagarumar zanga-zanga a ƙasar a wannan Juma’ar, lokacin da za a yi jana’izar mutanen da suka mutu a harin tagwayen bama-baman.

Jagoran addinin Iran, Ayatullah Ali Khamenei, ya yi alkawarin ɗaukar fansa mai tsanani kan tagwayen hare-haren.

Khamenei ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar bayan harin a ranar Laraba.

Jagoran addinin ya ce ”Muggan maƙiyan al’ummar Iran sun sake haddasa wani bala’i tare da kisan gilla ga al’ummar Kerman.”

“Da  yardar Allah za mu mayar da martani kan wannan bala’in da aka jefa al’ummarmu.”

A ranar Alhamis ministan harkokin cikin gidan Iran, Ahmad Vahidia, ya rage adadin waɗanda suka rasu a harin zuwa 84, wanda da farko hukumomi suka ce adadin ya kai 103.

Shugaban hukumar agajin gaggawar Iran, Jafar Miadfar, ya ce da farko an ƙirga wasu gawarwaki sama da sau ɗaya, saboda tarwatsewar da suka yi, kafin daga baya a gano hakan.

Harin shi ne mafi muni da aka kai cikin Iran a tsawon shekaru 45 a tarihin ƙasar ta Jamhuriyar Islama.

Leave a Reply