Ƙungiyar ILO ta horas da masu ruwa da tsaki a kan tsaron sana’o’i, kawar da bautar da yara a aikin haƙo ma’adinai a Neja da Osun

0
19
Ƙungiyar ILO ta horas da masu ruwa da tsaki a kan tsaron sana'o'i, kawar da bautar da yara a aikin haƙo ma'adinai a Neja da Osun

Ƙungiyar ILO ta horas da masu ruwa da tsaki a kan tsaron sana’o’i, kawar da bautar da yara a aikin haƙo ma’adinai a Neja da Osun

A ƙoƙarinsu na ganin an kawo ƙarshen bautar da ƙananan yara ke yi a Najeriya, ƙungiyar da ke kula da manya da ƙananan wurare haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ta gudanar da taro daga 18 zuwa 27 ga watan Feburailu na shekarar 2025 a jihohin Niger da Osun.

Manufar taron dai ita ce ƙarfafa guiwar masu ruwa da tsaki tare da wakilai daga cikin gwamnati, ma’aikata daga ƙungiyoyi tare da shuwagabannin yankunan domin kawo ƙarshen aikin bautar da yara ke yi a wuraren.

Hakazalika, an baiwa mambobin kwamitin da ke sanya ido kan ayyukan bautar da yara na jihohin da kayan aiki da za su taimaka wajen sanya ido, da kuma kai rahoton duk wani aiki na bautar da yara ƙanana.

Daraktan ƙungiyar kwadago ta Najeriya, Dr. Vanessa Phala, wacce ta samu wakilcin mai kula da ayyuka na kungiyar ACCEL Africa, Mrs.Celine Oni, ta bayyana cewa an yi wannan taron bitar ne domin ƙarfafa masu ruwa da tsaki tare da cibiyoyin da ke yaƙi da bautar da yara kanana, sannan ta jaddada cewa za a aiwatar da dokoki da tsare-tsare da za su taimaka wajen kawo karshen wannan matsala.

Ƙudurin karfo na shirin ACCEL Africa shi ne, aiki tare da hukumomi irinsu Ma’aikatar kwadago da bunkasa ayyukan yi ta kasa, da Ma’aikatar noma, Ma’aikatar da ke kula da ma’adanai da dai sauransu.

Na biyu shi ne, ɗaukar mataki kan musabbabin bautar da yaran ke yi ta hanyar samar da mafita bayan samun damar gudanar da bincike a yankunan da ake haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, sannan za a mai da hankali sosai kan muhimman fannonin samar da kariya, kuɗaɗe, kiwon lafiya da samar da aikin yi ga matasa.

Daraktan ta jaddada cewa za a magance dalilin haddasa wannan aiki na bautar da yara, wanda ta ce talauci da rashin samun kariya ne kan gaba wajen haifar da wannan matsala.

Controller na ma’aikatar kwadago da bunkasa ayyukan yi ta kasa reshen jihar Neja, Hauwa Zakariyya, ta ce, “samar da tsaro da kuma kiwon lafiya hakki ne da ya rataya a wuyan kowa, sannan ba za a samu wata ci gaba ba ma damar babu tsaro, don duk wasu munanan al’amura za su iya faru wa a wuraren aiki idan har ba a dauki matakin kare kai a lokacin da mu ke tsaka da aiki.

“Don haka ne ma mu ke daukar wannan kungiya ta ACCEL Africa da muhimmanci, wacce ta mai da hankali kan wuraren haƙar ma’adanai manya da ma kanana, domin kare kai daga mummunan al’amari makamancin abin da ya faru a yankin Kuchiko, inda aka rasa rayuka da dama da su ka hada da kananan yara.

Mun yi imanin cewar wannan tsari zai ilimantar da masu hakar ma’adanai yadda za su kare kansu anan gaba”.

Ana shi ɓangaren, Controller na ma’aikatar ƙwadago reshen jihar Osun, Mr.Solomon Ayinde Alabi, ya bayyana matukar farin cikinsa kan wannan aiki a jihar, duk da cewa jihar Osun ba ta gajiyar shirin ba na farko, amma dai shirin zai amfane su kamar yadda ya amfani sauran jihohi kamar Ondo da Neja wanda aikin ya kawo sauyi mai kyau.

Ya ce, “ɗaya daga cikin amfanin wannan shirin shi ne, rahoton da ke fitowa daga yankin Ibala.

Muna murna da cewa, rahoto ya tabbatar da cewa ficewar yara daga makarantu ya ragu sosai. Wannan babban labari ne gare mu a irin waɗannan yankuna”.

“Ina kuma yin kira gare mu a matsayinmu na iyaye, masu kulawa, da al’umma da mu yi amfani da wannan dama da kyau wajen ƙara azama wajen yaƙi da ta’addanci, bautar da yara a yankunan mu”.

KU KUMA KARANTA:Muna taya al’umman musulmai zagayowar watan azumin Ramadan — MƊD

A yayin taron bitar, wadanda suka halarci taron sun ziyarci wuraren haƙar ma’adanai a jihohi mabanbata don duba yadda ake gudanar da ayyukan, inda suka yi arba da kayan aikin kamar na’u’rori, tare da gano haɗarin da ke tattare da wannan aiki.

A cikin tattaunawa da Lawali Yusuf mai shekaru 13 cikin yara masu haƙar ma’adanai a Korokwa da ke Minna na jihar Neja ya ce, “ina wannan aiki ne saboda iyaye na ba su da karfin daukar nauyin karatuna, don haka na yanke shawarar yin wannan aikin saboda na tara kudi na fara zuwa makaranta kamar sauran abokaina. Nasan aikin hakar ma’adanai yana da matuƙar haɗari, amma bani da wata mafita bayan aikin”.

A yankin Idoka da ke Osun, shi ma wani dan shekara 11 me suna Ibrahim da ke hakar ma’adanai ya ce, “burina shi ne zama mai hakar ma’adanai idan na girma, don haka ne ma na zo nan a matsayin yaron gida.

Ina so na koyi yadda ake hako zinari duk da ma dai sau da dama ana korata daga wurin, sai dai ina dawowa saboda muradina kenan zama mai haƙar ma’adanai”.

Wannan taro dai ana tunanin cewar zai kawo sauyi wajen yaƙi da bautar da yara musamman a ɓangaren haķar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

Leave a Reply