Ƙungiyoyin Fulani makiyaya sun yi gagarumin taron neman bakin zaren dawo da martabar su a idon duniya daga kashin kajin da wasu ke shafawa mu su.
Ƙungiyoyin sun gudanar da taron ƙarƙashin ƙungiyar MIYETTI ALLAH a Abuja inda dukkan masu ruwa da tsaki suka halarta. Taron ya nesanta dukkan Fulani daga ayyukan ta’addanci da nuna za a iya samun miyagu a kowace ƙabila.
Fulanin sun yi ƙira ga gwamnati ta riƙa haɗa kai da ƙungiyoyin Fulani wajen samar da maslaha.
Wakilin Lamiɗon Adamawa Dr. Abubakar Umar Girei ya ce in an ba su dama za a iya kawo ƙarshen fitinar ɓarayin daji a arewa “A gwada mu ko na mako ɗaya ne a wata ƙaramar hukuma za a ga sauyi”
KU KUMA KARANTA:Najeriya ta samu tallafin dala biliyan 1.3 Don ƙarasa hanyar jirgin ƙasa daga Kano zuwa Nijar
Shi ma Shugaban ƙungiyar matasa makiyaya “JAM NDER FULBE” Kwamred Ahmad Muhammad Lamiɗo ya ce su na ɗaukar dukkan matakan raba baragurbi a matasan daga miyagun ƙwayoyi.
Gamayar ƙungiyoyin makiyayan ƙarƙashin jagorancin, Baba Usman Ngelzarma, da tsohon gwamnan Bauchi, Isa Yuguda, ta karrama shaharerren malamin Islama, Musa Yusuf Asadussunnah da sarautar Arɗon Adalci don yadda ya ke wayar da kai ga fahimtar da al’umma halin da makiyayan ke ciki.
Asadusunnah ya nanata ƙiran haɗa kai a arewa don salama mai ɗorewa.
A nan Fulanin sun buƙaci rushe dukkan ƙungiyoyin sa-kai da kan ɗauki mataki ba tare da dogon bincike ba.